Dalilin da yasa muka samar da tallafin Naira biliyan 200 ga ƙananan masana’antu da masu sana’o’i – Tinubu

President Bola Tinubu 1 1 750x430

Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa gwamnati ta samar da tallafin Naira biliyan 200 domin taimaka wa ƙananan masana’antu da masu sana’o’i wajen bunƙasa harkokinsu da ƙarfafa kasuwanci.

Tinubu, wanda mataimakinsa, Kashim Shettima, ya wakilta, ya bayyana haka a taron shekara karo na 31 kan Tattalin arzikin Najeriya da ƙungiyar kula da tattalin arzikin Najeriya ta shirya a Abuja.

Ya ce gwamnati ta ga muhimmancin tallafawa masana’antu da masu sana’o’i domin magance matsalolin da ke hana ci gaba.

Shugaban ƙasa ya bayyana cewa tattalin arzikin Najeriya ya samu ci gaba mai ma’ana, inda aka samu ƙaruwa a haɓakar GDP da kaso 4.23 cikin ɗari a watan Satumba, lamarin da ya nuna nasarar gyare-gyaren tattalin arziki da gwamnatinsa ke aiwatarwa.

Ya ce matakan da gwamnati ta ɗauka sun kasance bisa nufin daidaita tsakanin bukatun jama’a da dabarun tattalin arziki, tare da tabbatar da cewa marasa galihu, matasa da masu rauni sun samu damar cin gajiyar shirye-shiryen gwamnati ta hanyar samun rance da tallafi.

Tinubu ya ƙara da cewa gwamnati ta buɗe hanyoyi domin matasa su iya samun tallafi, rance da jarin haɗin gwiwa har zuwa dala dubu 100 domin bunƙasa kasuwancinsu da ƙirƙiro sabbin hanyoyin samun ci gaba.

Karanta: Ƙungiyar NUPENG ta ayyana Sanata Adams Oshiomhole a matsayin wanda ba ta maraba da shi saboda suka da ya yi wa PENGASSANYa ce wannan tallafi na biliyan 200 zai taimaka wajen magance kalubalen masana’antu da ƙarfafa gasa a tsakanin su.

Ya bayyana cewa fadada tsarin bayar da ƙananan rance ta hanyar internet ya ƙara haɓaka shigar jama’a cikin harkokin kuɗi, tare da taimaka wa ƙananan ‘yan kasuwa wajen samar da ayyukan yi a matakin al’umma.

Ya kuma gode wa ‘yan Najeriya bisa haƙurin da suke nunawa yayin da ake aiwatar da gyare-gyare, yana mai cewa kwanciyar hankalin kasuwar musayar kuɗi ba ta faru a banza ba, illa sakamakon ƙwarewa da tsare-tsaren gwamnati.

Shugaban ƙasa ya bayyana cewa tattalin arzikin ƙasar ya haura daga Naira tiriliyan 309.5 a 2023 zuwa Naira tiriliyan 372.8 a 2024, inda kuma kudaden shiga suka ƙaru zuwa Naira tiriliyan 27.8 a watan Agusta 2025.

Ya ce wannan nasara ta sa kamfanonin duniya irin su Fitch da Moody’s suka ƙara darajar kuɗin Najeriya saboda hangen nesa da tsare-tsaren tattalin arzikin gwamnati.

Haka kuma, Tinubu ya ce kudaden da ake samu daga fannonin da ba na mai ba sun ƙaru da kaso 411 cikin ɗari, inda harajin da ake tattarawa ya kai kashi 13.5 cikin ɗari na GDP, daga kashi 7 cikin ɗari a baya.

Ya ce dokokin gyaran haraji huɗu da ya sanya hannu a kansu za su taimaka wajen rage dogaro da man fetur, da sauƙaƙa biyan haraji ga kamfanoni da ƙarfafa fasahar sadarwa.

Shugaban ƙungiyar NESG, Mista Olaniyi Yusuf, ya bukaci gwamnati ta tabbatar da tsaro a ƙasar domin samun nasarar aiwatar da gyare-gyaren tattalin arziki, yana mai cewa babu ci gaba ko zuba jari idan babu zaman lafiya.

NAN

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here