Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shiga ganawa da gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele a fadarsa, Aso Rock da ke Abuja.
Wannan na zuwa ne awanni kadan bayan da kotun koli ta yi hukunci a ranar Laraba don yin watsi da wa’adin 10 ga watan Faburairu na daina amfani da tsoffin kudi.
Tawagar alkalai bakwai na kotun karkashin jagorancin mai shari’a John Okoro ne suka yanke hukunci kan karar da gwamnatocin Kogi, Kaduna Zamfara suka shigar.
Kotun kolin ta ce, gwamnatin tarayya da CBN dole su dakatar da batun daina amfani da tsoffin kudi har zuwa lokacin da kotun za ta sake duba batun a ranar 15 ga watan Faburairu.
Karin bayani na nan tafe…











































