Tsohon Babban Hafsan rundunar sojin ƙasa, Laftanar Janar Abdulrahman Dambazau, ya yaba wa jami’ai da dakarun Brigade ta uku ta rundunar sojin ƙasa ta Najeriya bisa hidimarsu ga ƙasa da jajircewarsu wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Jihar Kano.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mataimakin daraktan hulɗar jama’a na rundunar soji a Brigade ta uku, Manjo Babatunde Zubairu, ya fitar a Kano.
Dambazau ya bayyana yabon ne a yayin bikin wasannin al’adu na rundunar soji ta yammacin Afirka da Brigade ta uku ta shirya a barikin Bukavu da ke Kano.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya rawaito cewa bikin, wanda ya nuna ƙarshen horon rundunar na shekarar 2025, ya haɗa da manyan jami’an soji masu aiki da waɗanda suka yi ritaya, iyalansu, wakilan sauran hukumomin tsaro da kuma al’ummar yankin da ke ɗaukar bakuncin rundunar.
Tsohon babban hafsan sojin, wanda ya kasance bako na musamman a bikin, ya bayyana cewa bikin ya nuna yadda Brigade ta uku ke ci gaba da riƙe al’adunta tare da cika nauyin da kundin tsarin mulki ya ɗora mata.
Ya kuma yaba da halartar manyan baki, inda ya bayyana hakan a matsayin alamar kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin rundunar da al’ummar yankin da kuma haɗin gwiwarta da sauran hukumomin tsaro.
Dambazau ya ƙara yabawa jami’ai da dakarun Brigade ta uku kan ƙwarewa, ladabi da jajircewarsu wajen tabbatar da tsaro a sassan Jihar Kano, inda ya jaddada cewa ayyukansu sun taimaka matuƙa wajen rage aikata laifuka da tabbatar da zaman lafiya.
Tun da farko, kwamandan Brigade ta uku, Birgediya Janar Ahmad Tukur, ya bayyana nasarorin da rundunar ta samu a fannoni na ayyukan tsaro, horo da gudanarwa a shekarar 2025.
Ya kuma jaddada cewa Brigade ta ci gaba da gudanar da ayyuka a ƙarƙashin Operation MESA domin yaƙi da ’yan fashi da sauran laifuka a ƙananan hukumomin Shanono, Tsanyawa da Gwarzo, yayin da ya girmama jami’ai da dakarun da suka rasa rayukansu a yayin gudanar da aiki.













































