Shettima ya isa Switzerland domin halartar taron tattalin arzikin duniya

Shettima arrived 750x430

Mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya isa garin Davos na ƙasar Switzerland a ranar Lahadi domin jagorantar tawagar Najeriya a taron shekara-shekara karo na 56 na dandalin tattalin arzikin duniya, wanda za a gudanar daga 19 zuwa 23 ga Janairu, 2026.

Mataimakin shugaban ƙasar ya isa Switzerland ne daga Conakry na ƙasar Guinea, inda ya wakilci Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a bikin rantsar da Shugaban ƙasa Mamadi Doumbouya a ranar Asabar.

Da isarsa, ministocin harkokin waje da na kasuwanci da zuba jari, tare da jami’an ofishin diflomasiyyar Najeriya a Switzerland, sun tarbe shi.

Taron shekarar 2026 ya nuna wani muhimmin mataki a harkar diflomasiyyar tattalin arzikin Najeriya a duniya, sakamakon kaddamar da gidan Najeriya a Davos karo na farko.

Gwamnatin tarayya ta kafa wannan rumfar ƙasa ta musamman a titin Davos Promenade domin zama cibiyar tattaunawa da ministoci, zaman tattaunawar zuba jari da kuma hulɗar al’adu tsawon lokacin taron.

Wannan cibiya ta samo asali ne daga haɗin gwiwar gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu, kuma za ta rika karɓar manyan taruka da zaman dabarun tattalin arziki a tsawon makon taron.

A yayin taron, Mataimakin shugaban ƙasa zai gabatar da hasashen tattalin arzikin Najeriya na shekarar 2026 ga manyan shugabannin siyasa da kasuwanci na duniya, tare da halartar zaman tattaunawa kan amfani da basirar wucin gadi ta AIq ƙididdigar quantum da fasahar halittu ta hanyoyin da suka dace.

Haka kuma, zai gudanar da ganawa ta kai-tsaye da shugabannin ƙasashe, manyan jami’an kamfanonin ƙasashen duniya da shugabannin cibiyoyin kuɗaɗen ci gaba na duniya domin ƙarfafa haɗin gwiwa da ke daidaita da ajandar Sabunta Fata “Renewed Hope” ta gwamnatin Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Ma’aikatar masana’antu, kasuwanci da zuba jari ta bayyana cewa Najeriya za ta gabatar da damar zuba jari a fannoni daban-daban da suka haɗa da albarkatun ƙasa masu ƙarfi, noma mai dorewa ga yanayi, da kuma fannonin kere-kere da na dijital, a matsayin wani ɓangare na kokarin farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here