Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Olayemi Cardoso, ya bayyana cewa bankuna 14 a ƙasar nan sun riga sun cika sabon sharadin kuɗaɗen babban jari da aka ɗora musu.
Cardoso ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da aka gudanar a ranar Talata a Abuja, inda ya kuma sanar da sakamakon zaman kwamitin manufofin kuɗi na CBN (MPC).
Ya ce kwamitin ya lura da yadda tsarin bankuna ya ci gaba da nuna ƙarfi, tare da mafi yawan alamu na kwanciyar hankali suna cikin ƙayyadadden mizani.
Ya ƙara da cewa, kwamitin ya yaba da ci gaban da aka samu a cikin shirin ƙarfafa kuɗaɗen bankuna, inda bankuna 14 suka kammala cikawa bisa sabon tsarin babban jari.
Don haka, ya jaddada bukatar bankunan su ci gaba da aiwatar da manufofi da shirye-shiryen da za su tabbatar da kammala shirin cikin nasara.
Cardoso ya kuma bayyana cewa, an kammala cire rangwamen da ake bai wa masu basussuka a baya, wanda ya taimaka wajen ƙara gaskiya, ingantaccen sarrafa haɗari da kuma dorewar tsarin kuɗi a bankuna.
Ya ce duk da haka, tasirin cire wannan rangwame ba zai kawo cikas ga kwanciyar hankali ko lafiyar tsarin bankuna ba.
A ranar 28 ga Maris, 2024, CBN ta sanar da ƙarin sabon adadin mafi ƙarancin babban jari ga bankunan kasuwanci da ke da lasisin ƙasa da ƙasa zuwa naira biliyan 500.
Wannan ya sa bankuna da dama suka sanar da shirye-shiryen tara kuɗi ta hanyoyi daban-daban, ciki har da siyar da hannun jari da kuma fitar da takardun bashi.
A watan Janairu, Zenith Bank ta ce ta tara naira biliyan 350.46 ta hanyar siyar da hannun jari domin cika buƙatar CBN.
Haka kuma, a ranar 4 ga Yuli, Guaranty Trust Holding Company Plc (GTCO) ta sanar da kammala siyar da hannun jari a kasuwar London Stock Exchange (LSE). A ranar 22 ga Yuli kuma, CBN ta bayyana cewa bankuna takwas kacal suka kai ga cika sabon sharadi.
NAN













































