Babbar Jojin Najeriya za ta rantsar da sababbin lauyoyi masu muƙamin SANs a ranar 29 ga Satumba

CJN Justice Kudirat Kekere Ekun

Babbar Jojin Najeriya (CJN), Mai Shari’a Kudirat Kekere-Ekun, za ta rantsar da sababbin lauyoyi 57 masu matsayin SAN a ranar 29 ga Satumba, 2025.

Rahoton kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya bayyana cewa bikin rantsarwar na daga cikin shirye-shiryen buɗe sabon shekarar shari’a ta 2025/2026 a kotun koli.

A cewar sanarwar da daraktan yada labarai na kotun koli, Dr. Festus Akande, ya sanya wa hannu, bikin buɗe shekarar shari’ar zai ƙunshi gabatar da jawabin “halin da tsarin shari’a ke ciki” daga Babbar Alkaliyar Ƙasa.

Jawabin zai bayyana ayyukan kotun koli da tsarin shari’a gaba ɗaya a shekarar shari’a ta 2024/2025.

Haka kuma, manyan masu ruwa da tsaki a harkar shari’a za su gabatar da jawabai, ciki har da Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Ƙasa, shugaban ƙungiyar manyan lauyoyi (BOSAN), da shugaban ƙungiyar lauyoyi ta Najeriya (NBA).

Jawaban za su yi tsokaci kan matsayin da sashen shari’a ke ciki da kuma kalubalen da yake fuskanta.

Rahoton ya kuma tuna cewa kotun koli ta tafi hutun shekara-shekara bayan kammala shekarar shari’a ta 2024/2025 mai albarka a ranar Litinin 21 ga Yuli, 2025.

Sanarwar ta ƙara da cewa dukkan shirye-shiryen buɗe sabuwar shekarar shari’a za su fara ne da ƙarfe 10:00 na safe a kotun koli, tare da rantsar da sababbin lauyoyin SANs da kuma gabatar da jawabai daga bangarori daban-daban na sashenshari’a.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here