Babban sifeton ‘yan sanda ya umarci da a kara karfafa tsaro a makarantu, cibiyoyin lafiya da sauran gurare dake kasar nan

IGP alkali
IGP alkali

Babban sifeton ‘yan sandan Najeriya, Usman Baba, ya bada umarnin kai jami’an tsaro makarantu, cibiyoyin lafiya da sauran gurare masu mahimman ci a fadin kasar nan

Bayanin haka na dauke cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, CSP Olumuyiwa, ya fitar yau Lahadi a Abuja.

Sanarwar tace, Baba ya kuma bada umarnin yin zagaye da binkice akai akai, domin dakile duk wani shiri na ta’addanci a kasar nan.

Sannan kuma ja kunnan jami’an na ‘yan sanda, da su nuna kwarewa, jajircewa da kuma bin dokokin aiki, ya yin gudanar da aikin su a fadin kasa baki daya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here