Gamayyar kungiyoyin darikar tijjaniyya sun bayyana goyon bayansu ga dankarar gwamnan jihar Kano a jam’iyyar NNPP, Abba Kabir Yusuf.
Shugaban kungiyar Majma’u Ahbabu Shiek Ibrahim Nyass, wanda kuma shine mai magana da yawun Shehu Mahi Khaliphan Sheik Ibrahim Nyass a Nigeria, Shiek Tijjani Sheik Sani Auwalu, jikan shehu Ibrahim Inyass ne ya bayyana hakan a taron manema labarai da suka kirawo ranar Laraba a Kano.
“Ni Shiek Tijjani Shiek Sani Auwalu, jikan shehu Ibrahim Inyass, Shugaban kungiyar “Majama’u Ahbabu Shiek Ibrahim Nyass ” ta kasa, kuma Shugaban kungiyar TIGMEN, sannan kuma ni nake magana da yawun Shehu Mahi Khalipahan Shiek Ibrahim Nyass a Nigeria.”
“Ina kira ga ‘yan uwana ‘yan darikar tijjaniyya da su fito mazansu da matan su a ranar Asabar mai zuwa, 18 ga watan Maris su zabe Abba Kabir Yusuf a matsayin gwamnan jihar Kano.”
“Saboda can-cantar sa da dacewar sa da kuma makomar al’ummar jihar Kano, Muna kuma barranta kan mu da duk wasu masu kayar tijjaniyya suna ba da sanarwar zabar wani dantakara wanda ba Abba Gida Gida ba, da sunan tijjanawa.” Inji Shi.













































