Kotu ta tsare tsohon Mataimakin Gwamnan jihar Imo a gidan yari

EX Imo deputy governor Gerald Irona
EX Imo deputy governor Gerald Irona

Kotun Majistare da ke zaman ta a Owerri a ranar Alhamis ta bayar da umarnin tsare tsohon mataimakin gwamnan Imo Gerald Irona a gidan yari.

Alkalin kotun, Uwargida C. N Ezerioha, bayan sauraron masu gabatar da kara da kuma lauyan da ake tuhuma, ta bayar da umarnin a tsare Irona a gidan gyaran hali na Owerri.

Lauyan tsohon mataimakin gwamna S.I Imo ya gabatar da kudirin a bada belin Irona bisa son ransa.

Imo ya ce idan har ba za a iya ba da belin tsohon Mataimakin Gwamnan a kashin kan sa ba, dan majalisar dokokin Imo, Frank Ugboma, mai wakiltar mazabar Oguta ya amince aba da shi beli.

Sai dai babban mai gabatar da kara, Sunday Ogbuji, ya ki amincewa da neman belin, yana mai cewa alkalin kotun ba ta da hurumin sauraren karar.

Baya ga haka, babban mai gabatar da kara ya ce daya daga cikin tuhume-tuhumen da aka fi so a kan tsohon mataimakin gwamnan shine cin amana da aikata laifuka.

Ogbuji ya ce alkalin babbar kotu ne kadai za ta iya bayar da belin Irona.

Bayan sauraron bangarorin, alkaliyar kotun ta bayar da umarnin kai tsohon mataimakin gwamnan a gidan yari.

A hukuncin da ta yanke, alkaliyar kotun ta amince da lauyan mai shigar da kara cewa ba ta da hurumin yin magana ko bayar da belin wanda ake tuhuma.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here