An ci tarar mutum Kusan Naira 700,000 kan kisan dan jarida

329249640 493909919373797 3567399350156557472 n
329249640 493909919373797 3567399350156557472 n

Wata kotu ta ci tarar wani mutum dala 900 kwatankwacin kusan Naira dubu 700 bayan da ya amsa laifin kisa amma ba da niyya ba, na wani dan jarida da ya yi fice wajen sukar gwamnati.

A watan da ya gabata ne John Williams Ntwali, ya rasu bayan da wata mota da ke gudun tsiya ta kade su a kan babur din da ake goye da shi.

Hukumomi sun ce lamarin hadari ne kawai, ba da niyya ya faru ba.

Kungiyoyin kare hakkin dan’Adam sun bukaci da a gudanar da bincike mai zaman kansa inda suka bayyana mutuwar tasa da cewa abar zargi ce.

Kungiyar Human Rights Watch ta ce daman tun a baya ana ta yi wa Mr Ntwali barazana da suka a kafofin yada labarai masu goyon bayan gwamnati a kan irin rahotannin da yake yi na binciken kwakwaf.

An gudanar da sharia’r ne a cikin sirri amma an gayyaci wasu ‘yan jarida a lokacin bayyana hukuncin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here