Wasu ‘yan bindiga da ba a kai ga gano su ba, sun kai hare wani masallaci dake Ughelli a jihar Delta da safiyar Juma’a, yayin da suka raunata masallata 11 tare da garkuwa da uku.
Wani mazuanin gurin da lamarin ya faru, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasa NAN cewa harin ya faru da misalin karfe 6.47 na safe, yayin da musilmai ke gabatar da sallar Asuba a babban masallaci dake Okoroda a kan titin Ughelli.
Mazaunin wanda ya bayyana sunan sa Larry, ya ce karar harbe harbe ce ta tashi mutanen unguwar daga barci, yayin da suka ji ihu daga cikin masallacin.
Yayin da aka tuntube, mai magana da yawun hukumar yan sanda, DSP Bright Edafe, ya tabbatarwa da kamfanin dillancin labarai na kasa NAN faruwar lamarin, sai dai bai tabbatara da zancin garkuwar ba, yace kawai mutum 11 ne suka sami rauninka.
“Yanzu na kirawo DPO na Ughelli kuma ya tabbatar min da cewa mutum 11 ne suka sami raunika yayin kai harin.”
“Yanzu haka mun fara binkice za kuma musanar da ku halin da ake ciki.”
“Sai dai zuwa yanzu bamu kai ga kama kowa ba, amma ina mai tabbatar muka da cewa zamu kama duk wadanda suke da hunnu wajin kai harin.” Injishi.












































