Ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya lashi takobin kawo karshen yuwa, fatara da talauci a Najeriya idan ya zama shugaban kasa.
Atiku ya faɗi haka a lokacin da yake ƙaddamar da kamfen din sa a garin Uyo babbar birnin jihar AkwaIbom.
” Yau muna ƙaddamar da kamfen ɗin mu na takarar shugaban kasa mai taken, ceto Najeriya daga tsananin talauci, yunwa da kuma tabbatar da haɗin kai tsakanin ƴan kasa baki ɗaya.
” Idan kuka zaɓi PDP, kun zaɓi jam’iyyar da za ta kawo karshen talauci da yunwa kwatakwata, sannan kuma za a samu haɗin kai da ƙarshen ta’addanci gaba ɗaya.
” Na rantse idan kuka zaɓi PDP a 2023, za ku koma makaranta, kuma kowa zai samu aikin yi.
Lokacin da PDP ta kafa gwamnati a Najeriya a 1999, kowa ya shaida, tattalin arziki ya bunƙasa, an samu walwala da cigaban arziki, amma tun zuwan APC a 2015, abubuwa suka tabarbare.
Tun daga ƙarshen watan Satumba, aka buga gangar soma Kamfen a faɗin ƙasar nan.
Jam’iyyu gaba daya kaf ɗin su sun fantsama cikin ruguntsimin neman ƙuri’un ƴan Najeriya, tun daga kauyuka har zuwa birane.
A babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja, a ranar Litinin an ƙaddamar da kungiyar mata magota batan ɗan takarar shugaban Kasa na APC wato Bola Tinubu.
A wurin ƙaddamar da kwamitin, shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya hori ƴaƴan jam’iyyar su tabbata sun zagaye kauyuka da biranen kasar nan kafa domin karkato da ra’ayoyin mutanr su zaɓi jam’iyyar













































