Ministan Sadarwa da bunkasa tattalin arziki na zamani Farfesa Isa Ali Pantami ya bayyana cewa an yiwa rayuwarsa barazana da hukuncin kisa sakamakon tsarin hada lambar shaidar zama dan kasa.
Ministan ya ce galibin wadanda ke yaki kan manufar yanzu sukai lakwas, inda ya yi nuni da cewa hukumar tantance sunayen mutane ta kasa ta samu cigaba sosai matuka.
Isa Pantami ya bayyana haka ne a taron tsara manufofin cigaban fasahar zamani karo na hudu wanda ake gudanarwa duk ranar 16 ga watan Satumba, wanda hukumar NIMC ta shirya a Abuja.
Ya ce, “Za mu iya samun daidaiton tattalin arzikin mu na zamani ne kawai idan muka inganta tareda karfafa wa ‘yan kasar gwiwa su yi rajista a cikin bayanan mu na kasa.
“Lokacin da muka fara aikin an yi wa rayuwata barazana saboda shigar da rajistar NIN da layuka suka bijire, na yi imani cewa babu wanda zai iya sarrafa rayuwata a duniya sai Allah Madaukakin Sarki.
La’akari da shekaru uku da suka gabata hukumar NIMC ta gudanar da aiki me wuyar shaani tareda cimma alkaluman rajista na kusan miliyan 90 da aka yi rajista a kasar.
“A lokacin da na karbi ragamar hukumar NIMC adadin cibiyoyin rajistar ba su kai 1,000 ba, amma a yau muna da sama da dubu 50 a yau.
“Mun kafa tareda tsara manufofin kasa sama da 19 kuma ana aiwatar da su duka Ayanzu wanda wannan abune da bai taba faruwa ba a tarihin Najeriya.” Inji Pantami











































