Gwamnatin tarayya ta sanar da dakatar da yin amfani da samfurin kasashen waje da masu fasahar dora murya a talla-tallace su ke yi a Najeriya.
Shugaban hukumar da ke kula da tallace-tallace ta Najeriya (ARCON), Olalekan Fadolapo, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.
Olalekan ya ce dokar zata fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Oktuba na shekarar 2022.
Sanarwar ta kara da cewa a wani yunkuri na habbaka fasahar masu dora murya na gida, ya zama dole a hana amfani da na kasashen waje, domin yin haka zai habbaka fasahar tasu da kuma tattalin arzikin kasa baki daya.












































