Hukumar kula da ingancin kayayyaki ta kasa SON, ta yi kira ga kamfanoni da masana’antu da su bada fifiko wajan sarrafa kayayyaki masu inganci daza su cimma matakin inganci na duniya.
Shugaban humakar mai kula da ingancin kayayyaki ta kasa, mallam Farok Salim, shine yai wannan kira ya yin wani ran gadi zuwa wasu masana’antu da ke Kano a ranar Alhamis.

Ya ce ziyarar tazama wajibi a wani yunkuri na tabbatar da ganin kamfanoni da masana’antu na cikin gida suna samar da kayayyaki masu inganci wanda zasu guga kafada da kafada da sauran kayayyaki na kasa da kasa a kasuwanni.
“Duk wani kayan da jama’a basu ga tambarin SON a jiki ba kar a siya, ban-ban cin kudi kadan sai ya jamaka matsala”
“ina kuma kira ga mutane dasu dinga siyan kayayyakin da aikai a Najeriya, saboda ba duk kayan waje ne suka fi na gida ba, kuma idon muna siyan kayayyakin gida, to muna habbaka tattalin arzikin kasar mu ne” Inji shi.
Ya kuma yabawa masana’antun wajan samarwa da jama’a aikin yi da suke ba dare ba rana.

Jaridar Solacebase ta rawaitu cewa kamfanonin da hukumar ta ziyarta sun hadar da Aspira Nigeria Limited, Ammasco International Limited, ABY Lubricant Nageria, Gerawa rice mill ldt, Popular Farms & Mills ltd, Al-Wabeel rice mill, Ilera Agro da kuma kamfanin Royal Foam Products Nig Ltd.
A karshen ran gadin hukumar ta SON, ta shirya taron masu ruwa da tsaki domin tattaunawa akan yacce za’a habbaka masana’antun, da kuma ingancin kayayyakin da suke yi.













































