Yanzu-Yanzu: ‘Yan bindiga sun Kara sakin wasu mutane 5 daga cikin wadanda aka sace a harin Jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna.

Train victims
Train victims

Har yanzu dai hukumomin tsaro da gwamnatin tarayya ba su tabbatar da faruwar lamarin ba, sai dai wani mamba a cikin tawagar da ke tattaunawa kan lamarin, Tukur Mamu ya shaida wa manema labarai cewa an sako mutanen ne a ranar Talata, 2 ga watan Agusta.

Ya bayyana sunayen mutane biyar din da aka saki da suka hadar da Farfesa Mustapha Umar Imam, wanda likita ne a asibitin koyarwa na Jami’ar Usman Dan Fodio da ke Sokoto da Akibu Lawal da Abubakar Ahmed Rufai da Mukthar Shu’aibu da kuma Sidi Aminu Shariff.

Mamu wanda ya ce ya taka rawar gani wajen sako mutanen da harin jirgin kasan ya rutsa da su, ya bayyana cewa ya ja baya ne saboda barazanar da ake yi masa, da mutuncin sa da kuma rashin samun goyon bayan gwamnatin tarayya.

Sai dai ba a bayyana ko an biya ‘yan ta’addan wani kudi domin su sako mutanen da aka sace ba.

Ya ce duk da sakin mutanen biyar din, har yanzu wasu mutanen 34 daga cikin wadanda abin ya shafa na can a tsare a dajin.
Jaridar Solacebase ta Turanci ta cika shekaru biyar
Rahotanni sun bayyana cewa akwai dan tsohon gwamnan mulkin soja na jihar Kano, Idris Garba, da matarsa ​​da ‘ya’yansa da wasu da dama.

Idan dai za a iya tunawa, tun a ranar 28 ga watan Maris ne wasu ‘yan bindiga suka tarwatsa titin jirgin, inda suka kashe wasu tare da yin awon gaba da fasinjoji da dama.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here