An kama wani wanda ake zargi da taimakawa wajen shigar da wani dan jarida da ba musulmi ba cikin birnin Makkah mai tsarki, wanda hakan ya saɓawa dokar haramta wa wadanda ba musulmi ba shiga birnin mai tsarki.
Jami’an Saudiyya sun sanar a yau Juma’a cewa ɗan jaridar kasar Isra’ila, Gil Tamari, wanda ya je Saudiyya don bayar da rahotannin ziyarar da shugaban Amurka Joe Biden ya kai a can, ya yi amfani da wannan damar ya shiga cikin birnin Makkah a ɓoye, ya zagaya tare da ɗaukar wani ɓangare na garin domin gidan talabijin na Channel 13 News.
Haskawar da a ka yi a tashar talabijin ɗin ya haifar da cecekuce da kuma gargadin cewa zai iya lalata alaƙar da ake gani na tsakanin Saudiyya da Isra’ila.
Saudi Arabia, cibiyar addinin Islama, ba ta amince da Isra’ila ba.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Makkah ya ce an kama wani dan kasar Saudiyya tare da mika shi ga masu gabatar da kara.
“Shi (dan kasar) ya yi jigilar dan jaridar da ba musulmi ba, wanda ke da shaidar zama dan kasar Amurka, zuwa cikin babban birnin kasar (Makka) ta hanyar da aka tanada ga musulmi, wanda ya saba wa doka.
“Duk masu shigowa cikin masarautar dole ne su mutunta kuma su bi ka’idoji, musamman wadanda suka shafi wurare masu tsarki.
“Duk wani cin zarafi za a dauke shi a matsayin laifin da ba za a amince da shi ba,” in ji jami’in ‘yan sandan.
Jami’in ya ce an kuma aika da karar dan jaridar “wanda ya aikata laifin” zuwa gaban kotu.













































