Wata kungiya mai fafutukar yaki da cin hanci da rashawa ta Wadata Media and Advocacy Centre (WAMAC) ta yabawa gwamnatin jihar Kano bisa rufe cibiyoyin bada horon kiwon lafiya 26 dake ayyukansu ba bisa ka’ida ba a jihar.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano ce ta bada umarnin rufe cibiyoyin bada horon kiwon lafiyar 26.
A wata sanarwar da Kungiyar ta WAMAC ta fitar tace, ‘’muna jinjinawa jajurcewar ma’aikatar lafiya ta jihar Kano bisa yadda ta tashi tsaye wajen ganin an ceto al’umma daga gurbatattun ma’aikatan lafiya.
‘’Mun bukaci gwamnatin jihar Kano da ta kasance cikin masu sa ido a harkar gudanar da shugabanci nagari da kuma yaki da cin hanci da rashawa ta hanyar toshe duk wani abu na cin hanci da rashawa kamar yadda wani shirin gidan rediyo mai suna ‘Dan Duma’ ya gudanar da wani bincike kan zargin cin hanci da rashawa a cibiyoyi daban-daban.
“Kungiyarmu tare da tallafin gidauniyar MacArthur, a cikin shekaru hudu da suka gabata, ta fara aikin bada horo kan yadda ake gudanar da binciken kwakwaf a aikin Jarida tare da wani Shirin Yaki da Cin Hanci da Rashawa domin inganta kyakkyawan shugabanci ta hanyar amfani da harsunan gida a gidajen rediyo goma sha biyu dake shiyoyin kasar nan shida.













































