Najeriya ta musanta zargin tallafawa juyin mulkin soja a Jamhuriyar Nijar

Foreign Affairs Minister 750x430

Gwamnatin Tarayya ta musanta zargin cewa ta goyi bayan yunkurin juyin mulkin soja da bai yi nasara ba a Jamhuriyar Nijar.

Karamin Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Ambasada Sola Enikanolaye, ne ya fitar da wata sanarwa a ranar Alhamis kuma ya raba wa manema labarai, inda ya musanta wannan zargi tare da cewa karya ce da aka yi domin yaudarar jama’a.

“Hankalin Ma’aikatar Harkokin Waje ya kai kan wasu zarge-zarge na karya da kage da ke yawo a shafukan sada zumunta, cewa yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba a Nijar yana da goyon bayan ECOWAS, kuma ta haka Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta amince da shi.

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta musanta wadannan zarge-zarge gaba daya, tare da bayyana su a matsayin marasa tushe, na Rashin gaskiya, kuma an yi su ne da nufin yaudarar jama’a da bata sunan Najeriya.”

Ministan ya bayyana Najeriya a matsayin kasa mai son zaman lafiya, mai kare tsarin mulkin dimokuradiyya, kuma ginshikin dimokuradiyya da kwanciyar hankali ba wai kawai a Yammacin Afrika ba, har ma a yankin Sahel da fadin nahiyar Afrika.

“Najeriya ba za ta taba goyon bayan rashin bin doka ko canza gwamnati ba ta hanyar ka’ida ba a ko’ina, ko wane ne ya shiga ko wacce kasa ce.”

“Don cire duk wata shakka, matsayar Najeriya a bayyane take, kuma sanarwar hukuma mai lamba MFA/PR/2026/220 ta ranar 30 ga Agusta 2026, gwamnatin Najeriya ta nuna damuwa kan lamarin da ke faruwa a Jamhuriyar Nijar. Mun yi kira da a dawo da zaman lafiya da tsarin mulki ta hanyar tattaunawa mai hada kowa a kasar makwabta.” in ji sanarwar.

Ministan ya ce Najeriya ta na damuwa matuka kan duk wani sauya gwamnati ta hanyar da ba ta bisa ka’ida ba.

“Mu da Nijar makwabta ne da ke da tarihi, dangantaka da al’ada iri daya. Abin da muke so shi ne zaman lafiya, tsaro, dimokuradiyya da ci gaba ga Nijar, yankinmu da Sahel baki daya.

Kamar yadda muka fada a sanarwar da muka fitar, yin amfani da karfi don warware sabani na siyasa ya saba da wannan manufar da kuma dadewar manufofin harkokin wajen Najeriya.

Ko da yake Najeriya cikakkiyar mamba ce a ECOWAS, ba daidai ba ne, mugunta ce kuma karya ce a ce Najeriya ta amince ko ta yarda da juyin mulkin soja.

Muna rokon jama’ar Najeriya a cikin gida da waje da su yi watsi da bidiyoyi da labarai da wasu ke yadawa a yanar gizo domin tayar da fitina,” in ji sanarwar.

Ministan ya ce Najeriya ta tsaya tsayin daka kan ka’idojin ECOWAS kan Dimokuradiyya da Mulki Mai Kyau da kuma ka’idar Tarayyar Afrika.

“Najeriya za ta ci gaba da aiki tare da ECOWAS, AU da sauran kasashen duniya domin kare dimokuradiyya, kare mulkin doka da kuma inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankinmu,” in ji shi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here