Ana tuhumar wani mutum da cin amanar kasa saboda lalata allunan tallan Tinubu

Kotu
Kotu

An kama wani mazaunin Jihar Katsina, Aminu Sanda, wanda aka fi sani da Nesta, kan zargin laifin cin amanar kasa, bayan da aka zarge shi da lalata allunan tallan yakin neman zaben Shugaba Bola Tinubu.

Tun da fari, rundunar ‘yan sandan Jihar Katsina ce ta gayyaci Sanda, inda daga baya aka tsare shi bisa zargin cewa ya cire allunan yakin neman zaben Tinubu, sannan ya fasa sakatariyar jam’iyyar APC ta Jihar Katsina, inda ake zarginsa da sace kudi har Naira miliyan 35.

Sai dai, Sanda ya musanta wadannan zarge-zarge da ake yi masa na cewa ya lalata allunan tallan Tinubu da kuma fasa sakatariyar APC ta Jihar Katsina don sace miliyan N35.

“Ta yaya zan kasance shugaban kungiyar Dikko/Tinubu Vanguard na jiha, wadda kungiya ce ta magoya bayan Shugaban Kasa, sannan kuma na wulakanta allunan ta hanyar cire su? Wannan bai yi ma’ana ba.”

Ya jaddada cewa ba shi da wata alaka da wadannan laifuka da ake zarginsa da aikatawa, sannan ya bayyana zargin a matsayin mara tushe.

Tawagar lauyoyinsa su ma sun kalubalanci zargin, suna masu jaddada cewa ya kamata zargin da ake yi wa wanda suke karewa ya kasance yana da cikakkiyar shaid, kuma a bi matakan shari’a na gaskiya maimakon tsawaita tsare shi da ‘yan sanda ke yi yayin da suke ci gaba da bincike.

Daga baya dauke shi zuwa Babban Hedikwatar ‘Yan Sanda da ke Abuja, kuma daga nan wata Kotun Majistare da ke Jiwa a Babban Birnin Tarayya ta tura shi gidan gyaran hali bisa zarge-zarge da suka hada da cin amanar kasa.

Tun farko ‘yan sanda sun tafi gaban Kotun Majistare suna neman umarni na musamman don tsare Sanda na tsawon makonni biyu don ba su damar bincikar zargin da ake yi masa.

Sai dai, lokacin da lauyoyinsa suka bayyana a kotu a ranar Talata don neman belinsa, a lokaci guda ‘yan sandan sun shigar da bukatar neman kotun ta tsawaita tsare shi da wasu makonni biyu, suna masu kafa hujja da bukatar karin lokaci don kammala bincikensu.

A wani mataki da ya haifar da sabuwar fargaba a tsakanin tawagar lauyoyin Sanda, Mai Shari’a Huzaifa Macchudo ya dage bayyana hukunci kan bukatar belin.

A cewar lauyoyin Sanda, matakin dage hukuncin na iya bawa ‘yan sanda damar samun karin lokacin tsare shi.

An dage shari’ar zuwa ranar 15 ga watan Satumba domin yanke hukunci kan bukatar belin da lauyoyin Aminu suka shigar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here