Jami’an Hedikwatar ‘Yan Sandan Shiyya ta 1 dake Kano sun kama Ali Alhassan Mohammed kan zargin damfarar neman aiki, sojan gona da takardu na jabu.
Kakakin Rundunar “yan Sandan Shiyyar, DSP Abdullahi Hussaini, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba a Kano.
Hussaini ya ce jami’an sashen binciken manyan laifuka na rundunar shiyyar ne suka kama wanda ake zargin bayan samun korafe-korafe daga jama’a.
Ya ce wanda ake zargin ya rika karbar kudi daga mutanen da ke neman aiki, yana yi musu alkawarin zai basu aikin gwamnati.
“Binciken farko ya nuna cewa wanda ake zargin ya rika bayyana kansa a matsayin Mataimaki na Musamman a Hukumar Ilimin Firamare ta Jihar Kano SUBEB.
Ya yi amfani da wannan matsayi na karya wajen samun amincewar masu neman aiki,” in ji Hussaini.
Jami’in hulda da jama’a ya ce sama da mutum 10 ne suka fito har zuwa yanzu domin ba da shaida a lokacin binciken.
Ya kara da cewa bincike ya nuna wanda ake zargin ya karbi sama da Naira 40,000,000 daga wadanda ya yaudara.
A cewar Hussaini, wanda ake zargin ya amsa cewa ya yaudari sama da mutum 20 tare da buga takardun daukar aiki na bogi.
“Ya amsa cewa shi da kansa yake bugawa tare da bai wa wasu daga cikinsu takardun daukar aiki na bogi a matsayin shaidar cewa an dauke su aiki” in ji shi.
Kakakin ‘yan sandan ya ce an kwato wasu daga cikin wadannan wasikun daukar aikin na karya a hannun wanda ake zargin a matsayin abin gabatarwa a kotu.
Hussaini ya ce wanda ake zargin yana hannun ‘yan sanda kuma za a kai shi kotu da zarar an kammala bincike.
Mataimakin Sufeto-Janar na ‘Yan Sanda mai kula da shiyya ta 1, AIG Garba Ahmed, ya gargadi jama’a da su guji biyan kudi ga duk wanda ya ce zai ba su aikin gwamnati.
AIG din ya bukaci jama’a su tabbatar da sahihancin duk wanda ke neman kudi a hannunsu da nufin ba su aikin gwamnati ko mukami. (NAN)











































