Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ta dakile yunkurin garkuwa da mutane a garin Garun Mallam da ke Karamar Hukumar Garun Mallam, inda ta ceto Sarkin Noman Kano, Alhaji Yusif Nadabo, daga hannun masu garkuwan.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan a madadin Kwamishinan ’Yan Sanda, CP Ibrahim Adamu Bakori, ranar Lahadi.
A cewar sanarwar, lamarin ya faru ne da misalin karfe 11:30 na daren ranar Asabar, 29 ga Agusta 2026, bayan rundunar ta sami kiran gaggawa cewa wasu da ake zargin ’yan fashi ne sun shiga garin suna harbe-harbe a iska.
Maharan sun yi garkuwa da Nadabo yayin harin, sannan suka harbi mazauna garin uku, masu suna Yusif Nasiru, Salisu Garba da Ibrahim Hassan.
Bayan samun kiran, an tura dakarun sintiri na musamman da hadin gwiwar jami’an yankunan makwabta zuwa gurin da abin ya faru.
Rundunar tare da hadin kan mazauna gari sun bi sahun maharan da suka gudu, bayan matsin lambar da jami’an tsaro da mutanen gari suka yi wa masu garkuwan ya tilasta musu barin mutumin da suka sace suka tsere, inda aka ceto Nadabo ba tare da ya ji rauni ba.
An garzaya da mutane ukun da suka jikkata da kuma basaraken zuwa Asibitin Koyarwa na Aminu Kano domin duba lafiyarsu.
Rundunar ta tura jami’an sintiri a cikin garin Garun Mallam da kewaye domin kwantar da hankula da kuma hana afkuwar wani harin, yayin da ake ci gaba da farautar wadanda suka gudu da kuma bincike kan lamarin.
Kwamishinan ’Yan Sanda ya yaba da saurin mayar da martani na dakarun ’yan sandan da mazauna garin Garun Mallam da na makwabta, tare da jinjinawa kungiyoyin sa-kai ta Vigilante kan jajircewarsu.
CP Bakori ya yi kira ga mazauna gari da su kwantar da hankulansu tare da bayar da sahihan bayanai da za su taimaka wajen kamo masu laifin, yana mai jaddada aniyar rundunar na kare rayuka da dukiyoyin al’umma a fadin Jihar Kano.












































