Hukumar Daukar Ma’aikatan Tsaro Civil Defence, Gidajen Gyaran Hali, Kashe Gobara da ta Shige da Fice ta Kasa (CDCFIB), ta sanar da wadanda suka yi nasara a tantancewar jiki da lafiya na daukar ma’aikata a baya-bayan nan cewa hukumar ta kammala aikin tantancewa da fitar da sunayen wadanda suka yi nasara a shirin daukar ma’aikata na 2024/2025.
A cikin wata sanarwa da Sakataren Hukumar, Janar Abdulmalik Jibril (mai ritaya) ya sanya wa hannu, hukumar ta ce duk wadanda suka yi nasara a bangaren Digiri, su ziyarci shafin hukumar na daukar ma’aikata a “https://recruitment.cdcfib.gov.ng” daga Litinin 31 ga Agusta zuwa Laraba 2 ga Satumba 2026, domin duba ko an zabe su don yin tantancewa ta baki.
Ga wadanda suka yi rajista da NCE, OND ko SSCE, sanarwar ta ce su ziyarci wannan shafin daga Litinin 7 zuwa Laraba 9 ga Satumba 2026, domin duba ko an zabe su don yin aikin.
Jibril ya ce hukumar ba ta taba ba, kuma ba za ta taba aika ta email ba, ya jaddada cewa duk wata sadarwa game da aikin daukar ma’aikata za a same ta ne kadai ta shafin hukumar.
Ya ce dole ne wadanda aka zaba su zabi wurin da ya fi kusa da su, tare da zabar rana da lokaci, sannan su fitar da wasikar gayyatar su, inda ya kara da cewa dole ne wadanda aka zaba su zo da shigar da aka kayyade a cikin wasikar gayyatar.
“Don kaucewa shakku, za a bai wa wadanda aka zaba ne kawai damar shiga wurin aikin,” in ji sanarwar.
Hukumar ta sake jaddada cewa dukkan tsarin daukar ma’aikata ba a biyan kudi kuma yana gudana ne cikin gaskiya.
Ta gargadi masu neman aiki da su yi watsi da duk wani mutum ko kungiyar da ke neman kudi domin aikin.
Hukumar ta roki dukkan masu nema da su lura da adireshin shafinta da hanyoyin sadarwa na hukuma domin samun sabbin bayanai, tana mai jaddada cewa duk wata sadarwa ta gaskiya za ta kasance ne kawai ta shafin hukumar.












































