An sace ‘yan Najeriya 7,825, an biya kudin fansa N7.8bn a shekara guda – Rahoto

Wani rahoto da kamfanin bincike na SBM Intelligence ya fitar ya bayyana cewa kusan mutane 7,825 aka sace a hare-haren sace-sace da al’amuran da suka shafi garkuwa da mutane guda 1,713 tsakanin watan Yulin 2025 zuwa Yunin 2026, yayin da aka bayyana cewa an kashe akalla mutane 1,142.

Rahoton, mai taken The Capture of the Kidnap Economy, ya kuma bayyana cewa an biya kudin fansa har Naira biliyan 7.8 a cikin lokacin da aka yi binciken.

Masana harkar tsaro sun yi Allah-wadai da bunkasar wannan kasuwanci na garkuwa da mutane don neman kudin fansa a kasar, suna masu gargadin cewa biyan biliyoyin naira ga kungiyoyin masu aikata laifi na kara ba su damar sayen makamai da kuma dorewar ayyukansu na ta’addanci.

A cewar SBM Intelligence, kudaden fansa da masu garkuwan suka nema sun ragu daga N48bn zuwa N22.9bn, yayin da ainihin kudaden da aka biya suka karu daga N2.56bn zuwa N7.78bn, lamarin da ya sa kudin da aka samu ya karu daga kashi 5.35 cikin dari zuwa kashi 34 cikin dari.

Rahoton ya danganta kashi 90 cikin dari na kudaden fansa da aka biya ga bangaren Jama’atu Ahlis Sunna Lidda’awati Wal-Jihad (Boko Haram), da aka ce ta karbi N7bn daga al’amura takwas kacal.

Ya ce manyan garkuwa da mutane biyu ne suka kwashe kusan daukacin kudaden, ciki har da kudin fansa na N5bn da aka ce an biya domin kubutar da mutane 416 da aka sace a Ngoshe na jihar Borno, da kuma N2bn na dalibai da ma’aikata 315 na makarantar St Mary’s da ke Papiri a jihar Neja.

SBM Intelligence ta ce satar jama’a da yawa lokaci guda ta zama babbar hanyar da masu garkuwa da mutane suka fi amfani da ita, inda jihar Zamfara ta samu bullar irin wannan sace-sace har guda 92, yayin da jihar Sakkwato ta samu guda 76 a daidai wannan lokaci.

Rahoton ya lura cewa sake bullar sace-sacen dalibai a makarantu, musamman lamarin na Papiri, ya yi da lahani mai yawa ga fannin ilimi, aikin gona da kuma amincewar jama’a ga gwamnati.

Haka kuma rahoton ya yi gargadin cewa biyan kudin fansa ba ya tabbatar da tsiran rayuwar wadanda aka sace, inda ya bayyana cewa a kalla a lokuta shida, an kashe mutanen da aka yi garkuwa da su bayan an riga an biya kudin fansa.

Ya ba da shawarar katse hanyoyin kudaden da ke dorewa da ayyukan ta’addanci tare da magance matsalolin tattalin arziki da ke samar da mutane masu shiga kungiyoyin masu aikata laifi.

“Ba tare da tsari mai hade da nufin kai hari kan riba da ake samu daga laifin da kuma tushen sa ba, Najeriya na cikin hadarin mayar da garkuwa da mutane ba kawai a matsayin masana’antar manyan laifuka ba, har ma da hanyar samar da kudade ga kungiyoyin da suka fi barazana ga daidaiton kasar.” In ji rahoton.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here