Hukumar Yaki da Masu Yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annuti (EFCC) ta bayyana cewa ta fara binciken wani mutum mai suna Haruna Yusuf bisa zargin boye kudaden kasashen waje daban-daban wadanda ba a bayyana su ba, wadanda Hukumar Kwastam ta kama a Filin Jirgin Sama na Kasa da Kasa na Mallam Aminu Kano.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin, hukumar yaki da rashawa ta ce kudaden, wadanda suka hada da dalar Amurka 73,000, fam na Ingila 15,957 da Riyal na Saudiya 827,800, an kama su ne yayin gudanar da binciken yau da kullum na fasinjojin da ke tsakanin ranar 8 da 12 ga watan Agusta.
Mukaddashin Kwantirolan Kwastam na Shiyyar Kano/Jigawa, U U Adamu, ya bayyana cewa a ranar 8 ga watan Agusta, jami’an kwastam sun kama wasu kaya da babu mai su a cikin jirgin saman Saudi Air, wanda ke dauke da Riyal na Saudiya 827,800 da dalar Amurka 53,300 da aka boye a cikin takalma.
Bayan kwanaki hudu, jami’an sun sake kama wani kaya na Haruna Yusuf, wanda ya zo a jirgin Ethiopian Airlines mai lamba ET941.
Ya bayyana cewa bincike na biyu ta hanyar amfani da na’urorin zamani ya nuna dalar Amurka 20,000 da fam na Ingila 15,957 da aka boye a cikin takalman wasanni.
Daga baya ne Adamu ya mika Yusuf da kudaden da aka kwato ga hukumar EFCC a madadin Hukumar Kwastam.
Sanarwar ba ta fito fili ta bayyana ko Yusuf shi ne mamallakin kudaden Riyal na Saudiya da aka kama ba tare da mai su ba.
Adamu ya ce wannan kamun ya nuna irin taka-tsantsan da jami’an kwastam ke yi wajen gano zirga-zirgar kudaden kasashen waje da ba a amince da su ba ta iyakoki. Ya kara da cewa Hukumar Kwastam za ta ci gaba da karfafa gwiwa tare da hadi gwiwa da EFCC da sauran hukumomi domin yaki da laifukan kudi.
Yayin da yake karbar wanda ake zargin da kudaden a madadin Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, Mukaddashin Daraktan Shiyya na EFCC a Kano, Friday Ebelo, ya ce rashin bayyana kudaden masu yawa ya saba wa Dokar Hana Safarar Kudade (Kariya da Haramtawa) ta shekarar 2022.
Ebelo ya bukaci matafiya da su bi dokar bayyana kudaden da suke dauke da su, inda ya bayyana cewa bayyana kudi ba ya jawo wani hukunci, kuma matsalolin shari’a na iya tasowa ne kawai daga asalin kudaden da ba a bayyana su ba.
Ya ce hukumar EFCC za ta gudanar da bincike na tsanaki tare da gurfanar da lamarin gaban kotu daidai da doka.












































