‘Yan bindiga sun yi garkuwa da Alkalin Babbar Kotu a Jihar Kebbi

Kebbi Map 750x430
Kebbi Map 750x430

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da Alkalin Babbar Kotun Jihar Kebbi, Mai shari’a Faruku Hassan Bunza.

Daga bayanan da aka tattara, an cewa ‘yan bindigar da ake zargi sun kai hari gidansa da ke kan titin Zogirma a Karamar Hukumar Bunza ta Jihar Kebbi da misalin karfe 12 na daren Lahadi.

Majiyoyi sun shaida wa wakilinmu cewa harin ya faru ne jim kadan bayan Mai Shari’ar ya dawo daga tafiya da ya yi zuwa Sokoto.

“Dawowarsa kenan daga Sokoto sai ‘yan bindiga suka shiga gidansa suka tafi da shi,” in ji majiyar.

Ya kara da cewa babu wanda aka cutar a cikin gidan yayin harin, amma ‘yan bindigan sun rika harbin bindiga a sama kafin su tafi da shi.

“Bayan faruwar lamarin, nan take muka kai rahoton ga hukumomin da suka dace, ciki har da shugabancin Babbar Kotun,” in ji shi.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan Sandan Jihar Kebbi, SP Bashir Usman ya tabbatar da faruwar lamarin ga jaridar Daily Trust.

Ya ce “Ina tabbatar muku cewa an yi garkuwa da Mai shari’a Faruku Hassan Bunza a gidansa da ke Bunza kusan karfe 12 na dare.”

Jami’in ya ce bayan samu rahoton garkuwar da shi, Kwamishinan ‘yan Sandan Jihar, CP Umar Muhammad Hadejia ya tura kwararrun jami’ai da na leken asiri domin ganin an ceto shi koshin lafiya.

“A yanzu maganar da nake yi muku, jami’anmu na gudanar da bincike a wuraren da ake zargi, ciki har da dazuka, domin tabbatar da ceto Alkalin da rai ba tare da an cutar da shi ba,” in ji PPRO din.

Wani babban jami’i a Babbar Kotun Jihar Kebbi wanda ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana shi a matsayin abin takaici ga bangaren shari’a.

“Ba ni da ikon yin magana a hukumance, amma wannan lokaci na takaici gare mu, jin cewa an yi garkuwa da daya daga cikin alkalanmu a gidansa abu ne mai matukar tada hankali,” in ji shi.

Ya kara da cewa shugabancin Babbar Kotun ya riga ya gana da shugabanin hukumomin tsaro na jihar domin duba yadda za a tabbatar da sakin Mai Shari’ar cikin gaggawa.

Har zuwa lokacin da ake hada wannan rahoto, babu wata kungiya da ta fito ta ce ita ta yi garkuwa da Alkalin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here