Ministan Ilimi, Dr. Ma’aruf Tunji Alausa ya yaba wa Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, kan manyan sauye-sauyen da gwamnatinsa ta kawo a fannin ilimi, musamman daukar malamai 8,588 don inganta ingancin koyo da koyarwa a fadin jihar.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Kakakin Gwamna, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Talata.
Da yake jawabi yayin mika takardun aiki ga sabbin malaman da aka dauka a rufaffen dakin taro na Sani Abacha da ke Kofar Mata a Kano, Ministan ya bayyana wannan mataki a matsayin wani babban ci gaba a yunkurin jihar na farfado da fannin ilimi da magance matsalar karancin kwararrun malamai a makarantun gwamnati.
Dr. Alausa ya ce daukar sabbin malamai 4,900 tare da shigar da malaman shirin nan na Better Education Service Delivery for All (BESDA) 3,688 karkashin shirin ABBA Gida-Gida na nuna jajircewar Gwamnatin Jihar Kano na fadada damar samun ingantaccen ilimi da inganta sakamakon koyo.
Ya cewa ci gaba da bunkasa fannin ilimi na da matukar muhimmanci ga ci gaban kasa, inda ya yaba wa Gwamnatin Jihar Kano kan baiwa fannin fifiko ta hanyar tsare-tsaren da za su yi tasiri ga al’ummomi masu zuwa.
A nasa jawabin, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana rarraba takardun aikin a matsayin wata babbar nasara a cikin kudurinsa na kaddamar da dokar ta-baci a fannin ilimi.
Gwamnan ya ce daukar malaman zai taimaka wajen cike gibin karancin kwararrun malamai a makarantun gwamnati da kuma kara inganta matsayin ilimi a fadin jihar.
Gwamna Yusuf ya tuna cewa gwamnatinsa ta ware kashi 31 cikin dari na kasafin kudin 2026 ga fannin ilimi, inda ya bayyana cewa wannan zuba jari na ci gaba da samar da sakamako mai kyau, inda Kano ta zamo jiha mafi fice a jarrabawar NECO ta bana.
Haka kuma, ya godewa ga Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu bisa dakatar da karin kudaden jarrabawar NECO da aka yi shirin yi a baya, inda ya bayyana matakin a matsayin abin jin dadi wanda zai sa ilimi ya zama mai saukin biya da kuma isa ga daliban Najeriya.
Gwamna Yusuf ya bukaci sabbin malaman da aka dauka da su kiyaye da’ar aikin koyarwa ta hanyar nuna kwazo, da’a da kuma kwarewa wajen gudanar da ayyukansu.
Da farko, Kwamishinan Ilimi, Gwani Ali Haruna Makoda, ya bayyana cewa daukar malaman na cikin manyan gyare-gyaren da gwamnati ke yi na farfado da ilimi a Jihar Kano da kuma tabbatar da cewa kowane yaro yana da damar samun kwararrun malamai.
Haka kuma, Shugaban Hukumar Ilimi ta Jihar Kano (SUBEB), Malam Kabir Yusuf Kabir, ya sake jaddada aniyar hukumar na goyon bayan manufofi da shirye-shiryen gwamnati da aka tsara don inganta ingancin ilimin firamare da sakandare a fadin jihar.













































