Gwamnatin Tarayya ta dakatar da shirin sake duba kudin rijista na jarrabawar Afirka ta Yamma (WASSCE) ta shekarar 2027 da kuma ta Kasa (NECO) da daliban Babbar sakandire ke rubutawa (SSCE)
Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da Darakta mai kula da harkokin yada labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar ilimi ta tarayya, Folasade Boriowo ta fitar a ranar Litinin a Abuja.
A cewar Boriowo, ma’aikatar ta janye wasikar da ta fitar a ranar 18 ga Yuni, 2026, wadda ta kunshi shirin daidaita kudin, domin a yi cikakken duba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki kafin a yanke hukunci na karshe.
Ta ce wannan yanke hukunci ya biyo bayan damuwa da ra’ayoyi masu amfani da suka fito daga jama’a kan shirin kara kudin.
Ta kara bayyana cewa an gabatar da shirin sake dubawar ne saboda yanayin tattalin arzikin da ake ciki yanzu da kuma hauhawar kudin gudanar da ingantattun jarrabawar kasa.
Ta bayyana karuwar kudin sufuri, tsaro, buga kayan jarrabawa, amfani da fasahar zamani, tabbatar da inganci da sauran ayyuka masu muhimmanci a matsayin dalilan da suka sa aka gabatar da shirin.
A cewarta, Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, ya ba da umarnin a dakatar da shirin na wucin gadi, bisa jajircewar gwamnatin tarayya wajen tsara manufofi dan kowa da kowa da tsari wanda ya dace.
Ta kara da cewa ma’aikatar za ta tattauna da hukumar dake shirya jarrabawa, ma’aikatun ilimi na jihohi, masu gudanar da makarantu, kungiyoyin iyaye, kungiyoyin kwadago da sauran masu ruwa da tsaki a fannin ilimi a matsayin wani bangare na sabon tsarin sake dubawa.
“Shirin sake duba kudin rijistar jarrabawa ba zai fara aiki ba, kamar yadda aka sanar a baya, har sai an kammala tsarin tattaunawa,” in ji ta.










































