NELFUND ta yi barazanar daukar mataki kan makarantun da ke kin mayar wa dalibai kudin karatunsu

NELFUND 750x430

Asusun Ba da Lamunin Karatu ga Dalibai (NELFUND) ya bayyana damuwa kan rahotannin da ke nuni da cewa wasu manyan makarantu na jinkiri wajen mayar wa dalibai kudin makarantar da suka biya, ko kuma kin mayar da su gaba daya, ga wadanda suka riga suka biya kafin a ba su lamunin NELFUND.

A cikin wata sanarwa da Darakta mai kula da harkokin sadarwa na Asusun, Oseyemi Oluwatuyi, ya sanya wa hannu, NELFUND ta ce Tsarin Ba da Lamunin Karatu, wanda gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta kafa, an yi shi ne domin daukar mataki kan cikas din da ake samu wajen biyan kudin karatu, ba don kara wa dalibai nauyi ba.

Asusun ya kuma nuna damuwa kan abin da ya bayyana a matsayin karin kudin makaranta da sauran caji da wasu makarantun suke ba bisa ka’ida ba, inda ya yi gargadin cewa irin wadannan ayyuka na rusa manufofin Tsarin Lamunin Karatu.

A cewar sanarwar, NELFUND na tattaunawa da makarantu da kuma hukumomin da abin ya shafi domin tabbatar da cewa daliban da suka cancanta wadanda suka biya kudin karatu kafin a ba su lamuni sun samu kudin da ya kamata a mayar musu.

Sanarwar ta ce: “Asusun Ba da Lamunin Karatu ga Dalibai NELFUND ya lura da damuwa kan rahotannin wasu cibiyoyin koyarwa da ke jinkirtawa ko kin mayar da kudin makaranta ga dalibai wadanda suka riga suka biya kafin a ba su lamunin da kuma karin kudin makaranta da sauran caji ba bisa ka’ida ba.

“Tsarin Lamunin Karatu, shiri ne na gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, GCFR, an kafa shi ne domin magance cikas na kudi domin karatun gaba da sakandare, ba don kara wa daliban Najeriya nauyi ba.

“NELFUND na tattaunawa da hukumomin da abin ya shafi domin tabbatar da an mayar da kudin da ya dace ga daliban da suka cancanta, kuma caji na cibiyoyi ya kasance mai adalci, a bayyane, kuma ya dace da manufofin Tsarin.

“NELFUND ta himmatu wajen kare muradun dalibai da kiyaye mutuncin wannan babban shiri na kasa.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here