Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ta ce nan ba da dadewa ba za ta shiga yajin aikin sai baba-ta-gani domin neman biyan bukatun su wata guda bayan ta dakatar da yajin aikin na watanni tara.
Dokta Lazarus Maigoro, shugaban ASUU na Jami’ar Jos ne ya bayyana hakan a wata sanarwa ranar Alhamis a Jos.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya tuna cewa kungiyar ta dakatar da yajin aikin na tsawon watanni tara a watan Disamba 2021.
NAN ta ruwaito cewa ASUU ta fara yajin aikin tun da farko saboda gazawar gwamnatin tarayya wajen magance duk wasu batutuwan da aka yi musu alkawari a cikin yarjejeniyar shekarar 2009 tsakanin Kungiyar da gwamnatin tarayya.
Maigoro ya ce kungiyar ba za ta yi kasa a gwiwa ba har sai an daukaka darajar ilimi a kasar nan.
“Tsarin martanin gwamnati game da batutuwa shine na saba alkawari.
“Mun gaji da yaudarar su kuma lokaci ya yi da za mu dauki mataki don haka muna so mu sanar da ‘yan Nijeriya cewa mun gaji da ganawar da ba ta da amfani da Ministan Kwadago, Babban Sakataren Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa (NUC), da Hukumar Albashi, Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, da dai sauransu.













































