Hukumomin tsaro sun kama kwamandojin Boko Haram bakwai da ISWAP da ake zargi, yayin da suke dawo daga aikin Hajjin 2026 a makon da ya gabata ta Filin Jirgin Sama na Umaru Musa Yar’Adua da ke Jihar Katsina.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya sanar da hakan a ranar Juma’a.
Mista Tunji-Ojo ya bayyana lamarin a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja jim-kadan bayan Shugaba Bola Tinubu ya sanya hannu kan Dokar Hukumar Kula da Bayanan Shaida ta Kasa NIMC ta 2026.
A cewar ministan, an dakatar da wadanda ake zargin a filin jirgin sama na Katsina a ranar Alhamis din makon da ya gabata, sannan aka mika su ga Hukumar Tsaro ta Farin Kaya DSS.
“cikin farin-ciki na ke sanar da ku cewa, ma makon da ya gabata a ranar Alhamis, an kama kwamandoji bakwai da aka sani na Boko Haram da ISWAP, a lokacin da suke dawowa daga Makka, a filin jirgin sama na Katsina, sannan aka mika su ga DSS,” in ji Mista Tunji-Ojo.
Ministan bai bayyana sunayen wadanda ake zargin ba, ko an sanya su a cikin jerin mutanen da ake nema tun kafin su tafi Saudi Arabiya ba, ko kuma yadda suka samu izinin tafiya. Bai kuma bayyana ko an tuhume su a kotu ba a baya. Bai bayyana ko sun yi tafiya da fasfo din Najeriya ba, ko kuma sun kasance a cikin jerin mutanen da ake sa ido a ciki ko wajen kasar ba.
Mista Tunji-Ojo ya danganta kama su da ci gaban da aka samu a tsarin shaidar dijital da na kula da iyakoki na Najeriya. Ya ce yanzu bayanan biometric na kasar na iya magana da na shige da fice da kuma dandalin tsaro na kasa da kasa.
“Wannan zai yiwu ne kawai saboda bayanan NIMC yanzu ya hadu da bayanan shige da fice, kuma yana magana ma da Interpol 24/7, muna kuma iya sarrafa shi ta atomatik,” in ji shi.
Ministan ya ce gwamnatin Tinubu ta gaji tsarin shaidar da ya kasance a warwatse wanda ya hana musayar bayanai tsakanin hukumomin gwamnati.
“Lokacin da Shugaban Kasa ya zo, muna da tsarin da ba a hada shi ba a cikin tsarin kula da bayanan shaida. A wancan lokacin, samun fasfo da samun lasisin tuki ba su da wata alakla da bayanan shaidarmu. Amma yanzu, ba za ka iya samun fasfo din Najeriya ba sai an ciro bayanan ka daga NIMC.”
Ya ce hada tsarin ya karfafa hadin gwiwa tsakanin bayanan gwamnati kuma ya inganta ikon kasar wajen gano mutanen da ake zargi da matsalar tsaro da ke kokarin shiga ko fita daga iyakokin Najeriya.








































