Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, a ranar Talata ya gabatar da rokon ‘Babu hujjar ci gaba da shari’a’ (No-case submission) a shari’ar da ake yi masa kan zargin laifukan da suka shafi tsaron kasa.
Lauyansa, Paul Erokoro SAN, ne ya bayyana hakan a gaban Mai Shari’a Joyce Abdulmalik ta Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, jim kadan bayan Hukumar Tsaro ta DSS ta kammala gabatar da shaidunta.
Lokacin da aka kira shari’ar, lauyan Hukumar, Oluwole Aladedoye SAN, ya sanar da kotu cewa masu kara ba za su sake gabatar da wasu shaidu ba kan shari’ar.
Aladedoye ce bisa hujjojin da aka gabatar zuwa yanzu, masu kara sun gamsu cewa sun gabatar da hujjojin da suka dace kan tuhume-tuhumen da ake yi wa El-Rufai.
Bayan haka, Erokoro ya sanar da kotu cewa bangaren masu kare zai gabatar da rokon No-Case Submission, yana mai cewa masu kara sun gaza gabatar da isassun hujjoji da za su tabbatar da tuhume-tuhumen da ake yi wa tsohon Gwamnan.
Ya nemi makonni biyu domin gabatar da bukatar, yayin da bangaren masu kara suka nemi makonni biyu domin mayar da martani.
Erokoro ya kuma nemi a sauya wasu daga cikin sharuddan belin da aka gindaya wa El-Rufai, yana mai cewa suna da tsauri kuma suna da wahalar cikawa.
Ya ce musamman sharadin samar da ma’aikacin gwamnati mai mataki na 17, wanda ya mallaki gida a Maitama ko Asokoro da kuma wasikun tantancewa da amincewa daga Majalisar Sarakunan Jihar Kaduna, suna da wahalar samu.
Sai dai lauyan DSS ya soki bukatar, yana mai cewa akwai ma’aikatan gwamnati da suka cika wadannan sharudda, kuma ya roki kotu ta yi watsi da ita.
A hukuncinta, Mai Shari’a Abdulmalik ta ki amincewa da bukatar sauya sharuddan belin.
Mai shari’ar ta ce akwai ma’aikatan gwamnati da ke da kadarori a wuraren da aka ambata.
Daga nan ta dage shari’ar zuwa ranar 22 ga Satumba domin gabatar da rokon No-Case Submission da kuma daukar mataki na gaba a shari’ar.
Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN) ya ruwaito cewa DSS ta gurfanar da El-Rufai bayan ya yi ikirari a wata hira da Arise TV cewa ya samu damar sauraron wata tattaunawar waya da ke da alaka dK Mai Bai Wa Shugaban Kasa Shawara Kan Tsaro, Nuhu Ribadu.
Tsohon gwamnan ya ce tattaunawar ta nuna cewa an ba jami’an tsaro umarnin kama shi.
Ya danganta hakan da abin da ya faru da shi a Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe a ranar 12 ga Fabrairu bayan dawowarsa daga Alkahira ta kasar Masar.
An gurfanar da El-Rufai a ranar 23 ga Afrilu bisa zargin datsar tattaunawar wayar da ake zargin ta shafi layin NSA ba tare da izini ba, inda ya musanta tuhume-tuhume biyar da aka yi masa.











































