Gwamnatin Tarayya ta karbi ‘yan Najeriya 270 da suka dawo daga Afirka ta Kudu

IMG 20260611 WA0038 750x430

Gwamnatin Tarayya, ta hannun Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), ta karbi ‘yan Najeriya 270 da suka dawo daga kasar Afirka ta Kudu karkashin shirin dawo da ‘yan kasa da ake yi a yanzu.

Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da shugaban ayyuka na Ofishin ta na Legas, Mr Mohammed Olatunde ya sanya wa hannu, wadda aka ba wa Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN) a ranar Alhamis a Legas.

Olatunde ya ce ‘yan Najeriyan da suka dawo, wadanda suka yi rajista don shirin kuma suka kammala matakan tantancewa da ake bukata, sun iso Filin Jirgin Sama na Murtala Muhammed da ke Ikejan jihar Legas a ranar Alhamis.

A cewarsa, jami’an NEMA, hukumomin gwamnati da masu ruwa da tsaki sun kasance a wurin don tarbar wadanda suka dawo da kuma taimaka musu wajen sake shiga cikin al’umma.

Ya ce Gwamnatin Tarayya ta samar da kayayyakin sufuri don kai wadanda suka dawo zuwa wurare daban-daban a fadin kasar.

Olatunde ya kara da cewa an samar da motocin asibiti da sauran taimakon lafiya na gaggawa ga wadanda ke bukatar kulawar likita nan take.

Fasinjojin sun kasance daga cikin mutane kusan 1,000 da ofishin jakadancin Najeriya a Afirka ta Kudu ya ce sun yi rajista don a dawo gida.

Jingin ceto na kamfanin Air Peace ne ya dakko wadanda suka dawo din daga Johannesburg da misalin karfe 10:25 na safe.

Mai rikon mukamin Babban Kwamishinan Najeriya a kasar Afirka ta Kudu, Ambasada Alexander Ajayi ne ya raka fasinjoji 268 daga Pretoria.

Shugaba Bola Tinubu ya amince da jirgin ceto 5 da Air Peace za ta gudanar don wannan aikin.

An yi wa wadanda aka ceto rajista tare tantancewa da suka iso kafin hada su da iyalansu.

Kwasowar ta biyo bayan karuwar yadda ake kin jinin bakin haure a kasar Afirka ta Kudu, inda rashin aikin yi ya wuce kashi 30 wanda ya haifar da kai hari ga ‘yan kasashen waje.

An gudanar da zanga-zangar adawa a manyan birane, inda kungiyoyi masu dauke da makamai na kirar gida suka yi tattaki a wuraren masana’antu suna neman a kori bakin hauren da ba su da takardun zama.

Tashin hankali ya kara dagule wa bayan wata kungiya ta ‘yan kasa ta ba da wa’adin karshe na jama’a yana mai cewa dukkan bakin haure marasa takardun zama su bar kasar kafin 30 ga Yuni.

Ko da yake Pretoria ta musanta wa’adin a matsayin wanda ba na gwamnati ba, sanarwar ta haifar da damuwa nan take, lamarin da ya sa wasu kasashen Afirka ciki har da Ghana, Malawi da Mozambique, suka fara nata shirin dawo da ‘yan kasa.

Ma’aikatar ta bayyana cewa an tsawaita wa’adin tantance ‘yan Najeriya masu sha’awar dawo gida da kansu har zuwa Lahadi, 14 ga Yuni 2026, don karbar wasu da abin ya shafa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here