Jam’iyyar APC ta barranta kanta da wani jerin sunayen ’yan takarar sanata da ake cewa na jam’iyyar ne da ke yawo a shafukan sada zumunta da wasu kafofin yanar gizo, inda ta bayyana shi a matsayin bogi.
Jam’iyyar ta ce sunayen da aka yi wa take da “Cikakken Jerin ’Yan Takar Sanatan APC Zuwa Yanzu” ba daga ita ya fito dlba, kuma ba daga gare ta yake ba a yi watsi da shi gaba daya.
Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da Sakataren Yada Labaran APC na Kasa, Felix Morka, ya fitar a ranar Alhamis a Abuja.
“Hankalin jam’iyyar APC ya tashi kan wata ‘Cikakken Jerin ’Yan Takarar Sanatan APC Zuwa Yanzu’ da ke yawo a shafukan sada zumunta da wasu lafofin yanar gizo.
Ya ce cewa wannan jeri na bogi ne, bai kuma fito daga jam’iyyar ba.
Jam’iyyar ta bukaci mambobinta, masu ruwa da tsaki, manema labarai da sauran jama’a da su yi watsi da wannan labarin.
Jam’iyyar ta sake jaddada cewa Kwamitin Gudanarwa na Kasa (NWC) na APC ne kawai ke da ikon sanar da jerin sunayen ‘yan takarar na zaben fidda gwani da sauran tsare-tsaren da kudin tsarin mulkin ya tanada, ta hanyoyin sadarwa da ya amince da su. In ji sanarwar.
APC ta yi gargadi kan yada bayanai da ba a tabbatar ba, inda ta lura cewa irin wadannan wallafe-wallafen na iya yaudarar jama’a, haifar da rudani, da lalata amincin tsarin dimokuradiyyar cikin jam’iyyar.
Wannan bayanin ya zo ne makonni bayan APC ta gudanar da zaben fidda gwani na sanatoci a yankuna daban-daban a watan Mayu 2026 kafin babban zaben 2027.
A zaben fidda gwanin, an samu sakamako da dama na manyan mutane, ciki har da tabbatar da wasu sanatoci masu ci da wasu gwamnoni da suka lashe tikitin sanata.
An kuma hana ’yan takara 47 takara, ciki har da Ben Murray-Bruce, tsohon sanatan da ya taba wakiltar Bayelsa ta Gabas, tare da Benson Agadaga.












































