Sarkin Kano na 16, Khalifa Muhammadu Sanusi II, ya dakatar da Dagacin kauyen Rikadawa a Karamar Hukumar Madobi, Malam Rabi’u Yusuf kan zargin da ake yi masa na badakalar sayar da fili.
Alhaji Ali Ibrahim Ahmad Matawalle da Wazirin Kano, Alhaji Sa’ad Shehu Gidado ne suka sanar da dakatarwar a lokacin sauraren korafe-korafen da aka gabatar wa Masarautar Kano a ranar Laraba.
Jaridar SolaceBase ta ruwaito cewa korafe-korafen sun zargi dan gidan hakimi, Isah Dahiru, da dagacin kauyen da aka dakatar, Malam Rabi’u Yusuf, da zargin sayar da gonaki mallaki marigayi Hakimin Madobi, Alhaji Sale Musa Kwankwaso, ba tare da ya sani ko izini shi ba.
Da suke jawabi a lokacin sauraren karar, wakilan Masarautar sun ce bincike ya nuna dagacin kauyen yana da hannu a ma’amalar da ba ta dace ba, inda suka bayyana aikin a matsayin cin amana da kuma cin zarafin iko da martabar Masarautar Kano.
Daya daga cikin wadanda suka kai korafin, Muddasir Dahiru, ya shaida wa Majalisar Masarautar cewa ya gabatar da karar ne bayan ya gano cewa dan gidan hakimin da dagacin kauyen sun riga sun sayar masa da wani bangare na gonar hakimin ba tare da samun izinin mai gonar ba.












































