Ofishin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya karyata wani shafin Instagram da ake yadawa mai suna @goodluck_ebelejonathan, inda ya ce na bogi ne kuma na sojan gona.
A cikin wata sanar da mai taimaka wa Jonathan kan harkokin yada labarai, Mista Ikechukwu Eze, ya fitar a ranar Juma’a, ya ce tsohon shugaban kasar ba shi da wani shafi a Instagram kuma bai taba budewa ba.
Eze ya ce an kirkiri shafin ne don yaudara kan shi yass ake canza yanayinsa akai-akai, yana nuna kansa a matsayin shafin magoya baya yayin da mafi yawan lokuta yake kwaikwayon tsohon shugaban da nufin yaudarar jama’ar da ba su sani ba.
“Muna son jama’a su sani cewa shafin wani lokaci yana nuna kansa a matsayin na magoya baya, amma mafi yawan lokaci yana kwaikwayon tsohon shugaban ne.
“An canza sunan mai amfani da shafin sau 13 har yanzu kuma muna sa ran Meta za ta dauki matakin da ya dace nan ba da jimawa ba,” in ji shi. (NAN)












































