Babbar Kotun tarayya ta sanar da ranakun da za ta fara hutu

federal high court abuja

Babbar Kotun Tarayya za ta fara hutun shekarar nan da muke ciki ta 2025 daga ranar 28 ga Yuli zuwa 16 ga Satumba.

Wata sanarwa da Daraktar yada labaran kotun, Misis Catherine Oby Christopher, aike wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN a yau Alhamis a Abuja, ta ce kotun za ta ci gaba da zama a ranar 17 ga watan Satumba.
A cewar Misis Catherine Oby Christopher, a lokacin hutun, rassan kotun a Abuja da Lagos da kuma Port-Harcourt, za su ci gaba da aiki a lokutan hutun.

“Saboda haka, masu shigar da kara za su kasance da ‘yancin tunkarar kotunan da aka lissafa a sama musamman ma wadanda ke kusa da su,” in ji ta.

Daraktar yada labaran ta kuma sanar alkalan da za su yi aiki a lokacin hutun da suka hada da: na Abuja da Mai shari’a Emeka Nwite da kuma M. S. Liman za su jagoranta.

Sai Lagos kuma Mai shari’a Deinde I. Dipeolu da kuma mai shari’a Musa Kakaki, yayin da a Port Harcourt kuma Mai shari’a P. M. Ayua da mai shari’a A. T. Mohammed za su jagoranci shari’u.

Ta ci gaba da cewa hutun ya kasance ne bisa tanadin doka mai lamba 46 da doka ta 4 (d) na dokokin babban kotun tarayya ta shekarar 2019.
Sanarwar ta kuma ce babban alkalin kotun, Mai shari’a John Tsoho, ya yi wa takwarorinsa fatan alheri da kuma yin hutun cikin walwala.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here