Tsawon karni da dama, Hawan Sallah ya kasance daya daga cikin al’adun gargajiya da al’ummar Kano ke dauka a matsayin abin alfahari, wanda yake samun halartar dubban masu kallo daga ko’ina cikin Nijeriya da ma wajen kasa. mahaya dawaki cikin launi-launi iri-iri, masu rike da sarautu na gargajiya, jami’an fada, da shugabannin al’umma. Inda suke nuna cika da tumbatsar tarihin wannan tsohon birnin.
Amma a ’yan shekarun nan, al’ummar garin Kano sun daina gani da jin farin cikin da Hawan Dawakin ke da shi, abin da ya sa mutane da yawa cikin bakin ciki da bacon rai.
Dakatar da Hawan Sallar ya samar da babban gibi a al’amiran al’adu na jihar, ga iyalai da dama, bikin ba wai taron al’ada bane kawai, alama ce ta hadin kai, tarihi, da alfaharin al’umma. ’Yan kasuwa na cikin gida, masu sana’a, masu horar da dawaki, da masu yawon bude ido suma sun dogara da bikin na shekara-shekara don samun harkokin kasuwanci da tattalin arziki.
An gudanar da bukukuwan al’adar ne a lokutan bikin Karamar Sallah da Babba, Hawan na nuna tsarin sarautar Kano na daruruwan shekaru.. Mahaya da ke sanye da kayan ado na al’ada suna yin tattaki a gaban Sarki, suna nuna biyayya da kiyaye al’adu da aka gada daga zuriya zuwa zuriya.
Duk da haka, damuwar tsaro da rikicin masarautar Kano da ya taso a ’yan shekarun nan sun sa hukumomi da cibiyoyin gargajiya daina gudanar da bikin akai-akai. Jami’an sun ce tsaron jama’a ya fi bikin al’adu muhimmanci, musamman a lokutan da tashin hankalin siyasa da zamantakewa ke karuwa.
Rashin gudanar da Hawan ya fi shafar matasa wadanda ba su taba samun damar ganin bikin da idonsu ba. Mazauna da yawa suna tunawa da farin cikin da dawakan da aka kawata, bugun ganguna na gargajiya, da taruwar bkii daga sassa daban-daban na kasar ke bayarwa.
Masana tarihi da al’adu sun yi gargadin cewa idan aka ci gaba da dakatar da shi na dogon lokaci zai shafi kokarin kiyayewa da isar da al’adun gargajiyar Kano ga al-ummomi masu zuwa. Suna cewa ko da yake tsaro yana da muhimmanci, ya kamata a nemi hanyoyin da za a kare da bunkasa al’adu.
Duk da dakatarwar, mazauna Kano da dama suna da kyakkyawan fata cewa Hawan zai dawo da kayatarwarsa lokacin da yanayi ya ba da dama. Shugabannin al’umma, masu sha’awar al’adu, da masu yawon bude ido suna ci gaba da bayyana bege cewa dawo da bikin zai sake nuna arzikin tarihin Kano kuma ya karfafa matsayinta a matsayin daya daga cikin manyan wuraren al’adu a Nijeriya.











































