Tsohon Gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi, da takwaransa na Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, sun isa hedikwatar Sakatariyar Jam’iyyar NDC ta kasa da ke Abuja.
Obi, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour a 2023 da Kwankwaso, wanda shi ma tsohon dan takarar shugaban kasa ne na jam’iyyar NNPP, sun isa cikin murnar magoya baya.
Ana sa ran shugabannin biyu da suka koma NDC daga jam’iyyar ADC za su gudanar da taron shawara da shugabannin NDC.












































