Dan majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar Ikeja, James Faleke, ya karbi fom din nuna sha’awa da na tsayawa takara a jam’iyyar APC a ranar Talata a madadin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu gabanin zaben shugaban kasa na shekarar 2027.
A ranar Talata, sakataren tsare-tsaren jam’iyyar APC na kasa, Suleiman Argungu, ya bayyana bude fara aikin sayarda fam din, inda kuma ya mika fom din nuna sha’awa dana tsayawa takara ga Faleke, wanda shi ne ya kafa kungiyoyin Tinubu Support Groups.
Karbar fom din da Faleke ya yi, da biyan kudin da ya kai Naira miliyan 100 a madadin shugaban kasa, ya nuna fara neman sake tsayawa takarar shugaban a hukumance.
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta sanya zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar tarayya a ranar Asabar, 16 ga Janairu, 2027, yayin da zaɓen gwamna da na ‘yan majalisun dokokin jihohi za gudana a ranar Asabar, 6 ga Fabrairun shekarar 2027.
Hukumar ta kuma sanar da cewa zabukan fidda gwani na jam’iyyu, ciki har da warware rikice-rikicen da suka shafe zaben, zai gudana daga 23 ga Afrilu, 2026, zuwa 30 ga Mayu, 2026.
Hukumar ta kara da cewa yakin neman zaze na shugaban kasa da na ‘yan majalisar tarayya zai fara a ranar 19 ga Agustan shekarar 2026, yayin da na gwamna da na majalisun jihohi zai fara a ranar 9 ga Satumban shekarar 2026.











































