Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunan Murtala Sule Garo ga majalisar dokoki domin tantancewa tare da amincewa da shi a matsayin mataimakin Gwamna.
Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Mustapha Muhammad, ya fitar, inda ya bayyana cewa matakin ya yi dai-dai da sashe na 191(3) na kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999 wanda aka yi wa kwaskwarima.
Matsayin na mataimakin gwamna ya zama babu kowa ne bayan murabus ɗin tsohon mataimakin gwamna, Aminu Abdulsalam Gwarzo, a ranar 27 ga Maris, din bana.
Sanarwar ta ce bayan tuntuba da masu ruwa da tsaki, gwamnan ya buƙaci majalisar ta gaggauta amincewa da nadin Garo domin cike gurbin.
Garo mai shekaru 48, gogaggen ɗan siyasa ne da ya shafe sama da shekaru 20 yana rike mukamai daban-daban, ciki har da Shugaban Tsare-tsare na jam’iyya a jiha, mai bai wa gwamna shawara, da kuma shugaban karamar hukumar Kabo.
Haka kuma ya taba zama Shugaban kungiyar shugabannin ƙananan hukumomi watau ALGON na Kano, sai muƙamin Kwamishinan kananan hukumomi da masarautu, da kuma ɗan takarar Mataimakin Gwamna na jam’iyyar APC a zaɓen 2023.
Nadin nasa na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin Kano na ƙarfafa shugabanci da inganta ayyukan gwamnati a jihar.











































