Sarkin musulmi ya naɗa jikan jikan Sardauna mai shekaru 23 a matsayin sabon magajin garin Sokoto

1774526963811.IMG 20260326 121138 871 750x430

Mai alfarma Sarkin musulmi kuma shugaban Majalisar koli ta harkokin addinin Musulunci a Najeriya, NSCIA, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya naɗa Alhaji Ahmadu Bello Danbaba mai shekaru 23 a matsayin sabon magajin garin Sokoto a ranar Alhamis.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya rawaito cewa sabon magajin garin Sokoto ya gaji mahaifinsa marigayi Alhaji Bello Danbaba, wanda shi ma jikan marigayi firayim ministan Arewacin Najeriya, Sir Ahmadu Bello Sardauna na Sokoto ne.

Marigayi Bello Danbaba ya fito ne daga zuriyar Alhaji Marafa Danbaba da Hajiya A’ishatu Ahmadu Bello, babbar ɗiyar marigayi Sardauna.

Mukamin magajin garin Sokoto mukami ne na gargajiya mai daraja, kuma yana daga cikin manyan masu ba Sarkin musulmi shawara a majalisar masarautar Sokoto.

Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya amince da naɗin jikan Sardauna tare da wasu mutane 20 da Sarkin musulmi ya naɗa a fadarsa da ke Sokoto.

Sarkin musulmi ya bukaci sabbin waɗanda aka naɗa su guji harkokin siyasa, su zama masu riƙon al’umma kamar iyaye, tare da ɗaukar wannan naɗi a matsayin ƙaddarar Allah.

Ya ƙara da cewa nauyin shugabanci na buƙatar ƙarin sadaukarwa da aiki ba tare da son kai ba, yana mai ƙarfafa su su cika abin da ake tsammani daga gare su.

Daga cikin waɗanda aka naɗa akwai Alhaji Ibrahim Isa, ɗan marigayi shugaban gundumar Gatawa, Sarkin Kudun Gatawa, Alhaji Muhammad Bawa, da ya rasu a hannun ‘yan bindiga, tare da wasu da dama da aka ba mukamai daban-daban.

NAN ya kuma rawaito cewa sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Bello Sifawa, ne ya wakilci gwamnan a wajen bikin, wanda ya samu halartar kwamishinan kananan hukumomi da harkokin sarauta, shugaban ma’aikatan gidan gwamnati, sarakunan gargajiya da sauran manyan baƙi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here