Hukumar NAFDAC ta kwace jabun magungunan zazzabin cizon sauro da kayan kwalliya masu darajar Naira Biliyan 3

NAFDAC seizes counterfeit cosmetics worth ₦37m in Abuja e1727804061393 750x430 (1)

Hukumar Kula da ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC) ta ce ta kwace sama da allurai miliyan 10 na jabun magungunan zazzabin cizon sauro da kayayyakin kwalliya masu darajar Naira Biliyan uku a Kasuwar Trade Fair da ke Lagos.

Daraktan bincike da aiwatar da doka na NAFDAC, Dakta Martin Iluyomade, ya sanar da manema labarai a ofishin hukumar da ke Apapa a ranar Litinin cewa an dauki matakin ne bayan samun sahihan bayanan sirri a ranar 3 ga Fabrairu.

Iluyomade ya ce jabun magungunan da aka gano sun hada da magungunan zazzabin cizon sauro, allurai na maganin malaria, wadanda aka haramta su kusan shekaru 15 da suka wuce a kasar nan, da sauran su.

Ya ce an kwashe manyan motoci takwas dauke da jabun magunguna da kayan kwalliya daga wani gini mai bene uku da ake amfani da shi a matsayin ma’ajiya ta kayan gyaran mota, tare da kama mutane hudu yayin da bincike ke ci gaba.

A cewarsa, masu safarar jabun magunguna sun kware wajen boye kayayyaki a wuraren da ba a saba tsammanin samun magunguna ba.

Ya ce magungunan da aka kwace daga ma’ajiya na iya kashe ‘yan Najeriya Miliyan Uku idan suka shiga kasuwa.

A cewar sa, NAFDAC karkashin jagorancin Farfesa Mojisola Adeyeye za ta ci gaba da aikin kawar da jabun kayayyaki da marasa inganci domin kare lafiyar al’umma.

Ya kuma tabbatar da cewa, hukumar ba ta amincewa da jabun magunguna, tare da bayyana cewa za a rushe kungiyoyin da ke safarar irin wadannan kayayyaki.

Iluyomade ya bukaci manyan masu rarraba magunguna da su rika saye daga kamfanonin da NAFDAC ta amince da su kawai, sannan ya bukaci ‘yan Najeriya su kai rahoton duk wani abu da ake zargi zuwa ofishin NAFDAC mafi kusa da su.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here