Hukumar Kula da ‘Yan gudun Hijira ta Duniya (IOM) ta ce akalla mutane 53, ciki har da jarirai biyu, ake fargabar sun mutu ko sun bace bayan wani kwale-kwalen roba da ke dauke da mutane 55 ya kife a gabar tekun Libya
Hukumar ta ce ‘yan Najeriya mata biyu ne kacal aka ceto yayin aikin ceto da hukumomin Libya suka gudanar.
IOM ta ce kwale-kwalen ya kife ne a ruwan sanyi na tsakiyar Tekun Bahar Rum, a arewacin garin bakin teku na Zuwara, a karshen mako.
A cewar IOM, daya daga cikin ‘yan matan Najeriya da suka tsira ta ce mijinta ya nutse ya mutu, yayin da dayan ta ce jariranta biyu sun mutu.
Wadanda suka tsira sun ce kwale-kwalen na dauke da ‘yan gudun hijira daga kasashe daban-daban na Afirka.
Kwale-kwalen ya tashi daga Zawiya da misalin karfe 11 na dare a ranar Alhamis, sannan ya fara shan ruwa bayan awanni shida kafin daga bisani ya kife.
Har yanzu ba a san inda matafiyan ke kokarin nufa ba, sai dai yawancin kwale-kwalen ‘yan gudun hijira da ke barin Libya kan nufi tsibirin Lampedusa na Italiya, wanda ke da nisan kilomita 350 daga Zawiya.
Kwale-kwalen robobin da ake yawan amfani da su ba su dace da irin wannan tafiya ba, kamar yadda kungiyoyin agaji na Majalisar Dinkin Duniya suka sha gargadi.
IOM ta ce wannan shi ne karo na baya-bayan nan na hatsarin jirgin ruwa da ya faru a cikin tsananin yanayin hunturu, inda ake fargabar karin hadurra da ba a rubuta su ba.
Kungiyar ta ce Libya ba kasa ce mai aminci ga ‘yan gudun hijira ba.
IOM ta ce har yanzu ‘yan hijira na fuskantar barazana, bayan gano karin manyan kaburbura da wuraren tsare mutane a gabashin kasar.
Bayan wani samame a wani haramtaccen wurin tsare mutane a Ajdabiya, bincike ya nuna cewa an tsare mutanen ne tare da azabtar da su domin tilasta iyalansu biyan kudin fansa.
Hukumar ta ce a Kufra ma, hukumomi sun gano wani wurin tsare mutane a karkashin kasa mai zurfin mita uku, inda aka sako ‘yan gudun hijira 221, ciki har da mata, yara da jariri dan wata daya.
Bayanan farko sun nuna cewa an tsare mutanen na tsawon lokaci cikin yanayi mara tsari.
Domin taimaka wa masu rauni a hanyoyin hijira, IOM na tallafa wa shirye-shiryen dawowa gida bisa son rai ga ‘yan kasashen waje.
A karshen watan Janairu, hukumar ta taimaka wa ‘yan gudun hijira ‘yan Najeriya 177 su koma gida ta jirgin jin kai.
A watan Janairu kadai, akalla mutane 375 aka ruwaito sun mutu ko sun bace a tsakiyar Tekun Bahar Rum, a cewar kundin bayanan IOM kan ‘yan hijira da suka bace.
Daga ranar 1 ga Janairu zuwa 7 ga Fabrairu, akalla ‘yan gudun hijira 781 aka tare, tare da mayar da su Libya, inda 244 aka mayar da su a makon da ya gabata.
Tun bayan kifar da tsohon shugaban Libya, Muammar Gaddafi, a shekarar 2011, kungiyoyin safarar mutane da fataucin bil’adama suka yawaita a kasar.
IOM ta ce har yanzu wadannan kungiyoyi na cin riba daga halin kunci na mutane ta hanyar tura su cikin teku a kan kwale-kwalen da ba su dace da tafiya ba.
Hukumar ta sake kiran a kara hadin gwiwar kasa da kasa da samar da hanyoyin hijira masu aminci da na doka.
IOM na aiki tare da hukumomin kasa da na yankuna domin karfafa hadin gwiwar ketare iyaka, rushe hanyoyin safarar mutane da kuma tallafa wa wadanda suka tsira.
(NAN)













































