Gwamnatin Tarayya ta fara biyan albashi da alawus-alawus na ƙungiyar ASUU

Morufu Tunji Alausa 678x430

Gwamnatin Tarayya ta fara aiwatar da muhimman bangarorin jin dadin ma’aikata da ke cikin sabuwar yarjejeniyar da ta sake tattaunawa da Kungiyar Malaman Jami’o’i ta ƙasa (ASUU).

Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, a cikin wani umarni da ya fitar ga shugabannin jami’o’in tarayya a ranar Litinin, ya sanar da karin kashi 40 cikin 100 na alawus (CAA) ga mambobin ASUU, wanda zai fara aiki daga ranar 1 ga Janairu, 2026.

Alausa ya jaddada kudurin Shugaba Bola Tinubu na tabbatar da walwalar malaman jami’a da kuma dorewar tsarin jami’o’i a kasar nan.

Ya bayyana cewa wasu daga cikin jami’o’in tarayya sun riga sun fara nuna karin kudin a cikin biyan albashin ma’aikata.

Ministan ya umarci dukkan jami’o’in tarayya da su tabbatar da cikakken bin umarnin, ta hanyar shigar da karin da aka amince da shi cikin tsarin biyan albashinsu domin dukkan malaman da suka cancanta su amfana.

Haka kuma, Alausa ya bayyana bukatar bin ka’idoji sosai wajen aiwatar da tsarin biyan alawus na (CATA), inda ya ce an riga an tanadi biyan kudin tare da fitar da takardar umarni daga Hukumar Kula da Albashi, Kudin Shiga da Albashin Ma’aikata ta Kasa (NSIWC), tare da saka shi cikin kasafin kudin shekarar 2026.

Ya bukaci shugabannin jami’o’i da su yi amfani da albarkatun da suke da su domin tabbatar da biyan CATA cikin gaggawa, bisa ka’idojin NSIWC.

A cewar Alausa, aiwatar da karin CAA da kuma biyan CATA a kan lokaci zai inganta yanayin koyarwa a jami’o’i, ya kara kwarin gwiwar ma’aikata, tare da inganta koyarwa, bincike da sakamakon ilmantarwa.

Ministan ya tabbatar da kudurin Gwamnatin Tarayya na cika dukkan yarjejeniyoyin da ta kulla da masu ruwa da tsaki a bangaren ilimi, tare da tabbatar da tattaunawa mai kyau, gaskiya, zaman lafiyar aiki da kuma ci gaba da inganta ingancin ilimi a Najeriya.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here