Gwamnatin Jihar Lagos ta yi gargaɗi kan ɗauka ko karɓar sarautun gargajiya ba tare da sahalewar hukuma ba, tana mai bayyana cewa duk wanda ya aikata hakan zai fuskanci kamawa da gurfanarwa gaban shari’a bisa Dokar Sarakuna da Hakimai ta Jihar Lagos ta shekarar 2015.
Kwamishinan Kananan Hukumomi, Harkokin Sarauta da Raya Karkara na Jihar Lagos, Bolaji Robert, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka fitar a Lagos, inda ya nuna cewa gwamnati ba za ta lamunci karya doka a harkar sarauta ba.
Kwamishinan ya bayyana yawaitar masu ayyana kansu a matsayin sarakuna ko masu rike da sarautu a matsayin lamari mara kyau, yana mai haddasa tashin hankali, rikice-rikice da ruɗani a tsakanin al’umma da kuma jawo matsaloli.
Ya bayyana cewa irin waɗannan sarautun da ba su da izini, musamman waɗanda ke amfani da laƙabi irin su Oba, Mai Martaba Sarkin Gargajiya ko Mai Girma Sarkin Gargajiya, duka haramun ne bisa doka.
Ya kara da cewa dokar shekarar 2015 ta fayyace hanyoyin da ake bi wajen cike guraben sarauta da kuma ba da izinin rike mukaman gargajiya, inda ya jaddada cewa ma’aikatarsa ce kaɗai ke da ikon amincewa da duk wata sarauta a Jihar Lagos.
Robert ya bayyana cewa wasu sashe-sashe na dokar sun haramta ɗaukar laƙabin sarauta ko amfani da kayan ado na sarauta ga duk wanda gwamnati ba ta amince da shi ba, ciki har da rawanin lu’u-lu’u, takalman lu’u-lu’u, sandunan sarauta da kuma bulalan doki.
Ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta shirya aiwatar da dokar baki ɗaya, tare da gurfanar da duk wanda ya karya ta, yana mai cewa duk wata sarauta da aka ba mutum ba tare da amincewar gwamnan jihar ba ba ta da inganci a gaban doka.
Kwamishinan ya yi gargadin cewa masu aikata hakan na iya fuskantar hukuncin daurin shekaru biyu a gidan yari, yana mai bayyana cewa irin waɗannan ayyuka cin mutunci ne ga tsarin sarauta da al’adun gargajiya na jihar.
Ya kuma yi kira ga mazauna jihar da su rika kai rahoton duk wani ba da sarauta ba tare da izini ba ga ma’aikatar ko hukumomin tsaro domin daukar matakin gaggawa, yana mai cewa hakan wajibi ne domin kare mutunci da darajar tsarin gargajiya da al’adun Jihar Lagos.
NAN













































