Zargin ta’addanci: Waɗanda aka ceto sun shigar da ƙorafe-ƙorafe kan Tukur Mamu – shaida daga DSS

Tukur Mamu 1 750x430

Jami’in bincike na hukumar tsaron farin kaya ta ƙasa DSS ya bayyana a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja cewa da dama daga cikin mutanen da aka ceto bayan harin jirgin ƙasa na Abuja zuwa Kaduna sun shigar da ƙorafe-ƙorafe kan Tukur Mamu, wanda ake tuhuma da shiga tsakani a tattaunawar ‘yan ta’adda.

Jami’in DSS ɗin, wanda ya bayyana a matsayin shaidar ƙara ta shida a shari’ar ta’addanci da ake yi wa Tukur Mamu, ya gabatar da wannan bayani yayin amsa tambayoyi a gaban alkalin kotu Mohammed Umar, a lokacin da lauyan kare wanda ake tuhuma ke masa tambayoyi.

A yayin shari’ar, lauyan kare ya nemi kotu ta tabbatar da ko akwai daga cikin waɗanda aka ceto, ciki har da matar kwamandan sojoji a Jaji, da suka kai ƙorafi ga DSS kan wanda ake tuhuma, inda shaidar ta tabbatar da hakan tare da bayyana cewa ƙorafe-ƙorafen an rubuta su a takarda.

Lauyan DSS ya nemi kotu ta takaita tambayoyin da za su iya bayyana sunayen waɗanda aka ceto ko shaidu, ganin cewa kotu ta riga ta bayar da kariya ga dukkan su, yayin da lauyan kare ya bayyana cewa sunayen da aka ambata ba shaidu ba ne a gaban kotu.

Shaidar ta bayyana cewa an yi hira da mutane shida daga cikin waɗanda aka ceto a lokacin bincike, kuma ba a yi hirar a gaban Tukur Mamu ba.

Haka kuma ta tabbatar da cewa sautin murya da aka gabatar a matsayin hujja wani ɓangare ne na tattaunawar da aka fassara tsakanin Mamu da ‘yan ta’adda, duk da cewa shaidar ba ƙwararre ba ce a fannin nazarin sauti.

A ci gaba da binciken, shaidar ta tabbatar da an yi hira da wasu manyan jami’an tsaro da na addini, ciki har da Sheikh Gumi da Janar Jalingo, amma ba a yi kowanne daga cikin hirarrakin a gaban wanda ake tuhuma ba.

Haka kuma an tabbatar da cewa bukatar da Mamu ya yi na a haɗa mambobin kwamitin shugaban hafsoshin tsaro domin fuskantar juna a hira ba a amince da ita ba.

Bayan kammala tambayoyi, lauyan DSS ya sanar da kotu cewa, an shirya rufe shari’ar ɓangaren ƙara, domin ba wa wanda ake tuhuma damar fara kare kansa, yayin da lauyan kariya ya bayyana cewa, an fi son a ɗauki sabon rana domin buɗe kariya ba tare da gabatar da roƙon cewa babu hujja ba.

Alkalin kotu ya ɗage sauraron shari’ar zuwa wani lokaci.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here