Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Kaduna, Alhaji Muhammad Rabiu, ya musanta rahotannin da ke yawo kan cewa an sace sama da mutane 100 masu ibada a wata coci da ke ƙaramar hukumar Kajuru a Jihar Kaduna, inda ya bayyana su a matsayin ƙarya tsagwaron ta.
Muhammad Rabiu ya bayyana cewa masu yaɗa wannan labari wasu ne da ke cin gajiyar rikici, waɗanda burinsu shi ne tayar da hankula a Jihar Kaduna da kuma rushe zaman lafiyar da ake samu a halin yanzu.
Bayan kammala taron majalisar tsaron jihar da aka gudanar a ranar Litinin, kwamishinan ya kalubalanci masu wannan zargi da su fito da sunaye da cikakkun bayanai na duk wanda ake ikirarin an sace.
Ya gargadi masu yaɗa jita-jita da su daina, tare da jaddada cewa doka za ta ɗauki tsauraran matakai kan duk wanda aka samu da yaɗa labaran ƙarya da ka iya tayar da hankulan jama’a.
A nasa bangaren, shugaban ƙaramar hukumar Kajuru, Dauda Madaki, ya bayyana cewa jami’an tsaro sun duba yankin Kurmin Wali inda ake zargin an kai harin, amma ba su samu wata shaida da ke nuna faruwar wani hari ba.
Dauda Madaki ya ƙara da cewa sun ziyarci cocin da ake cewa an yi satar mutanen a cikinta, kuma ba a gano wata alama ta farmaki ba, yayin da hakimin yankin, Mai Dan Zaria, ya tabbatar da cewa babu irin wannan lamari da ya faru a al’ummar.
Ya kuma bayyana cewa jagoran matasan yankin, Bernard Bona, ya sanar da ‘yan jarida cewa babu wani abu makamancin hakan da ya faru, tare da nuna cewa har yanzu babu wanda ya kawo ko suna ɗaya na wanda ake zargin an sace, lamarin da ke nuna yunƙurin tayar da tarzoma a tsakanin jama’a.
Kwamishinan tsaron cikin gida da harkokin gida na Jihar Kaduna, Sule Shuaibu SAN, ya bayyana cewa shugabannin addinai ma sun bincika lamarin tare da tabbatar da cewa labarin ba shi da tushe.
NAN












































