Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya jagoranci taron majalisar zartarwa na farko a shekarar 2026, inda ya nuna ci gaba da ƙudurin gwamnatinsa na aiwatar da shugabanci nagari da bunƙasa ci gaban da zai dore a faɗin jihar.
Wannan bayani ya fito ne a cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya sanya wa hannu, wadda ta bayyana muhimman batutuwan da aka tattauna a taron.
Taron, wanda shi ne zama na 37 tun bayan kafa wannan gwamnati, ya gudana ne a gidan baki na gwamnan jihar Kano da ke Abuja, inda mambobin majalisar zartarwa suka halarta domin duba harkokin mulki da ci gaban jihar.
A yayin taron, gwamna Abba Kabir Yusuf ya nuna cewa gwamnatinsa na ƙara mai da hankali kan walwalar al’umma tare da hanzarta aiwatar da ayyukan ci gaba a dukkan sassan jihar Kano.
Gwamnan ya yaba wa mambobin majalisar zartarwa bisa jajircewarsu da ƙoƙarin da suke yi wajen aiwatar da manufofi da shirye-shiryen gwamnati da nufin inganta rayuwar al’ummar jihar, tare da ƙarfafa su su ci gaba da aiki tare domin cimma manufofin gwamnati.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa taron majalisar zartarwar na farko na shekarar ya gudana ne a daidai lokacin da ake yada raɗe-raɗin siyasa game da yiwuwar gwamna Abba Kabir Yusuf sauya sheƙa daga jam’iyyarsa ta NNPP zuwa jam’iyyar APC.













































