An harbe diyar tsohuwar Iya Oloja a Ibadan 

Gunmen 2
Gunmen 2

A ranar Laraba ne wasu ‘yan bindiga suka harbe diyar tsohuwar Iya Oloja ta Ibadan, marigayiya Alhaja Aminat Abiodun a gidanta da ke unguwar Bashorun a birnin.

An ce ‘yan bindigar da suka kai farmaki gidanta da ke unguwar Bashorun, Bodija, Ibadan, jihar Oyo, sun harbe Fatima har lahira.

An tattaro cewa ‘yan bindigar sun bar gidanta ne bayan sun tabbatar da cewa ta mutu kuma ba su dauke komai a gidan ba.

Wata majiya daga dangin, wacce ta nemi a sakaya sunanta, ta bayyana hakan ga manema labarai ranar Laraba.

“An kashe ‘yar uwarmu ‘yar marigayiya Iya Oloja Abiodun a Basorun da ke yankin Bodija a Ibadan.

“An kai harin ne a gidanta ba tare da wani dalili ba, ganin cewa Fatima mai son zaman lafiya ce.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda a jihar, Adewale Osifeso, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce za a bayar da cikakken bayani kan lamarin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here